KORONA: Mutum 422 sun kamu, mutum daya ya mutu ranar Talata

Hukumar NCDC ta bayyana cewa Najeriya ta samu karin mutum 422 da suka kamu da cutar korona sannan mutum daya ya mutu ranar Talata.

Idan ba a manta ba a ranar Litini mutum 420 ne suka kamu sannan mutum 8 sun mutu.

Zuwa yanzu mutum 249,154 ne suka kamu an sallami mutum 220,195 sannan mutum 25,873 na dauke da cutar.

Cutar ta yi ajalin mutum 3,086 a kasar nan.

Yaduwar cutar.

Legas – 97,157, Abuja-27,769, Rivers-15,881, Kaduna-11,042, Filato-10,223, Oyo-10,127, Edo-7,601, Ogun-5,779, Kano-4,874, Akwa-ibom-4,615, Ondo-4,998, Kwara-4,408, Delta-5,072, Osun-3,123, Enugu-2,824, Nasarawa-2,675, Gombe-2,695,

Katsina-2,399, Ebonyi-2,048, Anambra-2,705, Abia-2,145, Imo-2335, Bauchi-1,896, Ekiti-1,960, Benue-2,109, Barno-1,577, Adamawa-1,136, Taraba-1,254, Bayelsa-1,303, Niger-1,137, Sokoto-810, Jigawa-648, Yobe-501, Cross-Rivers-744, Kebbi-458, Zamfara-348, da Kogi-5.

Shugaban kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO Tedros Ghebreyesus ya ce karancin maganin rigakafin cutar korona na daga cikin matsalolin dake ci gaba da sa ana rasa mutane, Talauci da durkushewar tattalin arzikin kasashen duniya.

Ghebreyesus ya ce a makon da ta gabata ne ƙasashen duniya suka fi samu yawan mutanen da suka kamu da korona. Muna kuma da masaniyar cewa akwai mutane da dama da suka kamu da cutar da ba a san da su ba musamman a lokacin hutun kirsimeti da Sabon shekara.

Ya ce karancin maganin rigakafin cutar ya sa wasu kasashe sun fara yi wa mutanen su allurar rigakafin cutar zango na hudu sannan wasu kasashen Basu da isassun maganin rigakafin da za su yi wa jami’an lafiya da wadanda suka fi zama cikin hadari rigakafi har yanzu.

Ghebreyesus ya ce kamata ya yi a haɗa hannu domin ganin an kawar da wannan matsala cewa yin haka ne kawai zai taimaka wajen daƙile yaduwar cutar.

Ya hori mutane da su ci gaba da kiyaye dokokin gujewa kamuwa da cutar tare da yin allurar rigakafin cutar domin dakile yaduwar cutar.