Ƴan bindiga sun dagargaza ginin Ofishin ‘yan sanda da bom, sun saki masu laifi dake tsare

‘Yan bindiga sun dagargaza ginin ofishin ‘yan sanda da bamabamai a Ihiala dake karamar hukumar Ihiala a jihar Anambra.
Mazauna kauyen Ihiala sun ce maharan sun dirka wa ginin ofishin ƴan sandan bam da misalin karfe uku na safiyan Laraba.
Da take tattaunawa da PREMIUM TIMES wata mazauniyar garin Uju Okafor ta ce karar bindiga da bama-baman da maharan suka rika harbawa sun firgita mutanen garin da suka farka cikin dare a gigice.
Uju ta ce sai da garin Allah ya waye tangararan sannan suke ji labarin cewa mahara ne suka kawo wa ginin ofishin ƴan sanda cikin dare.
Shi ko Chinonso Okoye ya kara da cewa maharan sun saki wasu masu laifukan da ke tsare a ofishin ‘yan sandan.
“Gabanin wayewar gari ne muka fara jin ruƙugin fitar harsashi da fashewar bambamai. Mun samu labarin cewa maharan sun saki wasu masu laifi dake tsare a ofishin.
Bayan haya kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Tochukwu Ikenga ya tabbatar da aukuwar haka a wani takarda da ya fitar daga ofishinsa.
Ikenga ya ce ‘yan sandan sun yi bata kashi da maharan har sai da suka fatattaka su.
“Dakarun sun kwace bindiga kirar AK-47 guda daya bayan maharan sun gudu.
“ Ba a rasa rai ko ɗaya ba sai dai fashewar bamabaman sun lalata ginegine da dama ciki har da ofishin ƴan sanda.
Sannan kuma ya tabbatar cewa maharan sun saki wasu fursunonin dake tsare a ofishin sai dai a lokacin da yake magana ya ce ba shi da tabbacin ko guda nawa ne suka arce.