Faston da ya halasta auren mace fiye da ɗaya a kiristanci ya roki yafiyar kiristoci, ya ce ya yi kuskure ne

Idan ba a manta ba a watan Satumba PREMIUM TIMES ta buga labarin wani faston darikan Angilika mai suna Lotanna Ogbuchukwu da ya halastaauren fiye da mace ɗaya a addinin Kirista.
Ogbuchukwu ya ce ya samu wahayin haka daga Allah sannan duk limamen cocin addinin kirista karya suke wa mutane domin Allah bai haramta auren mace fiye da daya ba.
A dalilin haka Ogbuchukwu ya ajiye aikinsa na fasto da cocin Angilika bayan ya yi aiki da cocin na tsawon shekara uku sannan ya bude nasa cocin domin wayar da kan mutane kan wai sakon Allah game da auren mace fiye da ɗaya.
A koyin da Ogbuchukwu yake yi ya yi kira ga maza su rika auren mace fiye da daya ka maimakon namiji ya ajiye farka, ya aure ta kawai ya fi.
Sai dai bayan watanni uku da fadin haka PREMIUMTIMES ta samu labarin cewa faston ya nemi afuwar cocin Angilika cewa kuskure ne ya yi fassarar wahayin da aka yi masa.
A wata wasikar da faston ya fitar da gidan jaridar ta samu Ogbuchukwu ya roki cocin da ta dawo da shi aikinsa domin ya tuba kuma ya dawo kan tafarkin Ubangiji da na cocin.
Ya ce daga yanzu zai gudanar da aiyukkan sa bisa ga umurin Allah da na cocin.
Ogbuchukwu ya kuma nemi afuwar duk mutanen da suka ji ba daɗi game da kalaman sa a wancan lokacin cewa ba zai sake yin haka ba.