ZARGIN TSAFI: Kotu ta gurfanar da mutumin da ya rataya shirgegen laya a kofar ofishin abokin aikinsa

Kotun majistare dake Ojo a jihar Legas ta gurfanar da Endurance Jagun ranar Litini bisa laifin rataya shirgegen laya a kofar shiga ofishin abokin gaban sa.
Kotun ta gurfanar da Jagun bisa laifin yi wa wani barazanar rayuwarsa da tada hankalin mutane.
Jagun ya musanta laifin da ake zarginsa da su a gaban alkali L J.k Layeni.
Lauyan da ya shigar da karar Simon Uche ya ce Jagun ya aikata haka ranar 27 ga Maris a Kamfanin China Civil Engineering Construction Corporation, LASU a Ojo.
Uche ya ce a wannan rana Jagun ya samu sabanin da Wani abokin aikinsa Adekunle Adeshina inda bayan haka wato bayan ya koma gida sai ya hado kulumboton sa ya ya rata shirgegen laya kofar shiga ofishin Adeshina.
Kotun ta bada belin Jagun akan naira 100,000 da gabatar da shaida daya a kotun.
Za a ci gaba da shari’a ranar 20 ga Mayu.