Kotu ta daure Enema da ya damfari Abubakar mai siyar da Zinari, gwal din naira miliyan 1.2 a kasuwar Wuse, Abuja

Kotun Grade 1 dake Kado a babban Birnin tarayyar Nigeria Abuja, ta yanke wa Alfa Enema mai shekara 30 hukuncin zama a kurkuku bayan ya saci sarkan zinare a wani shagon siyar da gwala-gwalai dake Abuja.
Kotun ta gurfanar da Enema bisa ga laifin cin amana, hada baki da damfara.
A kotun Enema ya musanta laifin da ake zarginsa da su.
Alkalin kotun Malam Muhammed Wakili ya yanke wannan hukuncin ne bayan wadanda suka shigar da kara sun ki amincewa da rokon bada belin Enema da bangaren da ke kareshi ta yi.
Wadanda suka shigar da kara sun ce har yanzu ‘yan sanda na gudanar da bincike domin kamo abokan satan Enema.
Wakili ya ce za a ci gaba da shari’ar ranar 23 ga Mayu.
A bayanin da lauyan da ke wakiltar masu kara a kotu Stanley Nwafoaku ya ce a ranar 24 ga Maris ne Wani Abubakar Abubakar mai siyar da gwala-gwalai a kasuwar Wuse ya kawo kara ofishin ‘yan sanda dake Wuse Zone 3.
“ Abubakar ya ce a ranar 20 ga Maris Enema tare da wasu abokan sa suka zo shagonsa inda suka siya sarkar zinare kirar 18 karat akan naira miliyan 1.2.
“ Abubakar ya ce a ranar Enema ya aika kudin ta wayarsa sannan kuma ya mika masa takardar takardan shaida cewa ya biya kudaden ashe buge yayi masa.
Nwafoaku ya ce bayan ‘yan sanda sun kama Enema ne suka gano cewa ya siyar da sarkar akan naira 463,000.
Lauyan dake kare Enema Goodness Ajinomoh ya roki kotun ta bada belin Enema cewa Enema ba zai gudu.