ZARGIN CIN AMANAR KASA: Obi ya ce sharri, bita-da-kulli da hassada ce ake yi masa don an ga ya lashe zaben 2023

Dan takarar shugaban kasa na LP Peter Obi ya yi suka ga kalaman da ake yadawa wai shi yana tunzurz mutane da ingizasu don Najeriya ta wargaje a nada gwamnatin rikon kwarya don ya fadi zabe.
Obi ya fadi a wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa wanda shi da kansa ya saka wa hannu, ya ce Kazafi, makirci, tuggu da hassada ce kawai ake yi masa amma ba zai taba ingiza wasu su kawo cikas ga kasa Najeriya ba.
Duk da cewa a kwanakinnan an bankado wasu maganganun sa da ya yi da ke nuna kiyayyarsa sa ga musulunci inda yake cewa zaben 2023 Jihadi ce tsakanin Musulmai da Kiristocin Najeriya, Obi ya musanta cewa shi ya so ya ci da addini ne a takarrasa na shugaban kasa.
“Ban taba tattaunawa ko kwadaitar da wani ko wasu su yi wa kasar Najeriya zagon kasa ba. Wadanda su ke yi suna yi don su bata min suna.
Zuwa yanzu dai Obi ya ce ya tattara hujjojin sa kaf kuma tuni ya garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon zaben da aka bayyana Tinubu na APC wanda yayi nasara.
A ranar Asabar da ta wuce an fallasa wani faifan murya, wanda ke ɗauke da wata tattaunawa tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi da kuma Shugaban Cocin ‘Living Faith’ na Duniya, David Oyedepo.
Faifan muryar dai jaridar People’s Gazette ce ta fallasa shi, wanda a cikin sa Obi ke roƙon Fasto Oyedepo ya taimake shi ya watsa saƙon sa ga Kiristocin Yankin Kudu maso Yamma da na wasu yankunan Tsakiyar Najeriya, ya na so ya sanar da su cewa su fito su zaɓi Peter Obi, domin zaɓen Obi “jihadin addini ne.”
Hakan ya nuna cewa Obi ya kira Oyedepo sun yi maganar kafin zaɓen 2023 kenan. Ga abin da faifan muryar ke ɗauke da shi a fassarar Hausa:
PETER OBI: “Daddy, ina so ka taimake ni ka yi wa mabiyan ka na Yankin Kudu maso Yamma da na Kwara, wato Kiristocin Kudu maso Yamma da na Kwara. Ka nuna masu cewa wannan (zaɓen) fa “jihadin Kiristoci ne.”
OYEDEPO: “Ni ma na yi amanna da haka ɗin. Na yarda da hakan. Na yarda hakan ya ke.”
PETER OBI: “Idan buƙata ta biya, to za ku taɓa yin da-na-sanin goyon baya na da ku ka yi ba.”