Zargin Fani-Kayode cewa akwai rubutun arabi akan takardar kudin Najeriya tun kafin mulkin mallaka karya ne – Bincike DUBAWA

Zargi: Tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Femi Fani-Kayode na zargin cewa kafin zamanin mulkin mallaka, akwai rubutun da aka yi da larabci a kan takardar kudin Najeriya.

Banbance-banbancen da ke tsakanin ‘yan Najeriya sun hada da banbancin kabila, da na addini da na harshe, wadanda kuma za’a iya cewa su ne suka hadu suka zama ginshikin albarkar al’adun da kasar ke takama da shi. Sai dai wata sa’a, wadannan bangarori na al’ummar kan sami rashin jituwa tsakaninsu.

Na tsawon shekaru da dama yanzu Najeriya ta fiskanci rigingimu sakamakon kishi, irin wanda ke haddasa takaddama tsakanin kabilu ta yadda kowanne bangare ke neman rinjaye a fagen siyasar kasar. Sai dai yawancin wadannan rigingimu ba komai ke janyo su ba illa labarai na karya da masu yaudarar jama’a. Wadannan labarai sukan fito daga ire-iren mutanen da ke da karfin fada a ji, kama daga shahararru a fagen fina-finai da wake-waken kasar zuwa malaman addini da ‘yan siyasa.

Ranar asabar 29 ga watan Mayu, Femi Fani-Kayode tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya ya wallafa wani sharhi a shafin shi na tiwita mai suna @realFFK mai cewa:

“Abu mai daukar hankali ne a ce takardar kudin nera tana dauke da rubutun da aka yi da harrufan larabci tun kafin mulkin mallaka. Yaya za’a fayyace hakan, kuma me wannan ke nunawa?”

Ya kuma hada wannan sako da hoton takardan kudin pam daya wanda Najeriyar ta taba amfani da shi.

Wannan sako ya kai ga ma’abotan shafin na sa na tiwita wadanda suka kai sama da millyan guda, kuma cikin sa’o’i shidda kacal mutane 294 suka mayar da martani dangane da batun, wasu 457 suka sake raba sakon sa’annan mutane 957 suka nuna alamar amincewarsu da batun.

Wannan sharhi dai ya sami yarda da goyon bayan ma’abotan shafin abin da ya kasance tubalin irin tsokacin da suka yi.

Misali Mahmud Zakariya (@MahmudZakariya4) ya ce: “Wannan ya nuna cewa yankin arewacin Najeriya tana da iko sosai fagen siysar kasar. Babu yankin da ya fi arewa mahimmanci”

Wani mai suna @Favbreed1 kuma cewa ya yi: “Yadda turawan mulkin mallaka na Burtaniya suka bari aka yi amfani da wadannan harrufa a takardun kudin kasar da ba ruwanta da addini ne ya baiwa Filani damar tunanin cewa Najeriya da jama’arta nasu ne kuma daidai ne a kore su daga matsugunnensu domin su mallaki filayensu na gado.”

Prince Stephen Blossom (@GraciousTongue) cewa ya yi: Wannan ya nuna cewa shugabannin kudun da ke takama sun waye kuma suna da illimi ko daya basu da wayo. Wannan ya gaya mun dalilin da ya sa kananan kabilu kamar na Filani suka iya daukar Najeriya a matsayin na su. Tun da wuri suke sanya burinsu sannan su cigaba da shirye-shiryen cimma wannan buri. Shi ke nan!

Wani mai goyon bayan sharhin, @topsy_adeusi shi ma ya yi tsokaci kamar haka: Rikicin da muke gani yau, kashi 85 cikin 100 Burtaniya ce ta haddasa. Arewa tana cikin talauci yayin da kudu ke cikin wadata. Sai Burtaniya tare da tallafin sarkin musulmi a Sokoto suka yanke shawarar mayar da jama’ar da ke sauran yankunan bayi. Dan haka ganin wadannan harufa ba wani abin mamaki ba ne. (saynotobritain)”

Fani-Kayode wanda aka fi sani da FFK mutumi ne wanda a ‘yan kwanakin nan ya yi ta yin irin furutan da basu da tushe yana dogaro da yawan jama’ar da ke samun labaran da yakan wallafa a shafukan shi na yanar gizo su yayata irin labaran. Akwai misalai da dama a shafukan DUBAWA.

TANTANCEWA

Domin tantance wadannnan zarge-zarge na Mr. Fani-Kayode Dubawa ta fara da bin tarihin Najeriya. Sakamakon binciken ya nuna cewa sabanin wannan zargi na tsohon ministan sufurin, babu ma takardar kudi kafin zuwan turawan mulkin mallakar. Idan aka ce kafin mulkin mallaka ana nufin kafin turawa suka fara mulkin kasar a shekarar 1914 lokacin da Birtaniya ta dunkule yankunan arewa da na kudu a waje daya a karkashin mulkin Birtaniya domin ta sauwake ayyukarta na tafiyar da kasa. Wannan dunkulewa ne ya tabbatar da girkuwar Najeriya a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

A binciken tarihin takardun kudi a Najeriya kuma, babban bankin kasar wato CBN ta ce:

“kafin mulkin mallaka kowace al’ada na da abinda take amfani da shi wajen siyayya, akwai wadanda suke amfani da wuri, abun hannu/warwaro, beads, kwalabe, gishiri, da suaran makamantansu.”

Wannan bayani da babban bankin kasa ta CBN ta yi, ya karyata wannan zargi na Mr. Fani-Kayode tunda dai ba’a ma amfani da takardun kudin a zamanin da yake ambata.

DUBAWA ta kuma sake tantance hoton takardar kudin da Mr. Fani-Kayode ya wallafa, inda ta gano kwanan watan da ke kan kudin ya nuna 15 ga watan Satumban 1958. Tabbas wannan kwanan wata bata kasance kafin zamanin mulkin mallaka ba ne yadda tsohon ministan ya bayyana.

Har wa yau sabanin zargin tsohon ministan, rubutun da yake zargi larabci ne ajamin Hausa ne inda ake amfani da harrufan larabci a rubuta abu a hausance. Shahararren dan jarida Mannir Dan Ali ya bayyana haka a wani labari da ya rubuta wa BBC. “Ajamin hausa ne ba larabci ba a kan takardun kudin,” dan jaridan ya rubuta.

“Rubutun Ajamin da ke kan kowane takardar kudin an yi su ne saboda dubbai da milliyoyin mutanen da ke amfani da harshen Hausa, wadanda irin haruffan da suka iya rubutawa da karantawa ke nan domin su ake amfani da su wajen koyarwa a makarantun arewa a wancan lokacin”

Mal. Dan Ali tsohon babban editan jaridar Daily Trust ya bayyana cewa asali ma Ajami ne aka fara amfani da shi wajen illimi da koyarwa a nahiyar Afirka. Karnoni da dama kafin zuwan turawan mulkin mallaka daga kasashen yamma da kiristoci ‘yan Mishan wadanda suka kawo harrufan Romawan da ake amfani da su yanzu.

Yawancin kasashen Afirka na amfani da Ajami, wasunsu sun hada da Swahili a yankin gabashin Afirka, da harsunan Najeriya irinsu Kanuri, Nufanci, Yarbanci, Filatanci, Hausa, Tamashek – ko kuma harshen da Abzinawa ke amfani da shi a yankunan arewaci da yammacin Afirka.

Musa Muhammad wani masanin tarihi ya ce lallai rubutun da ke kan takardar neran, Hausa ce aka rubuta da harrufan na ajami “Harrufan da ke kan takardar kudin nerar ba ruwansu da addini kamar yadda su ma harrufan Romawan ba ruwansu da addini duk da cewa su ake amfani da su wajen rubutu a Bible ko kuma littafi mai tsarkin kiristoci. Duk wani harshen da aka rubuta da harrufan larabci muna kiransu Ajami,” a cewarsa.

Wani malamin sadarwa a jami’ar Maiduguri, Abubakar Mu’azu ya ce alamun da ke kan neran na nuna darajar takardar kudin ne a Hausa.

“Harrufan Arabin da aka yi amfani da su wajen rubutun hausa ana kiransu Ajami. Balarabe zai iya karantawa amma ba zai san abin da rubutun ke nufi ba sai dai in yana jin hausa,” ya fadawa Dubawa.

Rubutun Ajamin da aka yi a takardar kudin da Mr. Fani Kayode ya sanya a shafinsa na Tiwita yana nufin “Pam Daya” a hausa wanda ke nufin “one Pound” a turance.

A Karshe

Zargin tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode na cewa akwai rubutun arabi/larabci kan takardar kudin Najeriya tun kafin mulkin mallaka karya ne. A zamanin da aka yi kafin mulkin mallaka babu takardun kudi. A wancan lokacin kowace al’ada na da abun da ta amince da shi a matsayin kudin sayayya wadanda suka hada da wuri, da abun hannu/warwaro, beads, kwalabe da gishiri.

Bacin haka, kafin mulkin mallaka ba’a riga an kirkiro Najeriya a matsayin kasa mai cin gashin kanta ba sai bayan shekara ta 1914 lokacin da gwamnatin Birtaniya ta girka Najeriyar a matsayin kasa lokacin da ta dunkule yakunan arewaci da kudancin.

Bincike ya nuna cewa rubutun ba arabi ba ne illa ajamin hausa na ba. Hakan ya karyata zargin Mr. Fani-Kayode.