Rumbun Ajiyar Kuɗaɗen Najeriya a Waje ya huje, saura dala biliyan 34

Duk da irin ƙarin farashin litar ɗanyej mai da aka samu a watannin baya, Babban Bankin Najeriya ya bayyana sauran kuɗaɗen ajiyar ƙasar da ke waje bai haura dala biliyan 34 ba.
Rabon da asusun ya yi ƙasa zuwa wannan adadin kuwa tun cikin watan Yuli, 2017, shekaru huɗu da su ka gabata kenan.
Tsakanin 31 Ga Mayu zuwa 10 Ga Yuli, asusun ya ragu da dala miliyan 222.3.
Kafin nan kuwa can baya a cikin Disamba, 2020 sai da asusun ya kai abin da ke ciki ya kai dala biliyan 36.5.
PREMIUM TIMES ts kira Kakakin Yaɗa Labarai na CBN, domin jin ƙarin bayani daga bakin sa, amma bai amsa kira ba.
Fito da ƙididdigar adadin raguwar asusun ya zo daidai lokacin da Gwamnonin Najeriya na jam’iyyar PDP su ka yi zargin cewa Gwamnatin APC ta maida NNPC kandami a sha a yi wanka, CBN ya koma rijiyar tsakiyar gari, sai kamfatar ruwan ciki gwamnatin APC ke yi kawai.
A wani sabon zargin yadda ake ta kamfata da jidar kuɗaɗe a ƙarƙashin gwamnantin APC, Ƙungiyar Gwamnonin PDP sun bayyana cewa manyan hukumomin tara kuɗaɗen gwamnatin tarayya sun zama wuraren da a kullum a ke ta yi wa dabdala da rubdugun wawurar kuɗaɗe.
A taron da gwamnonin na APC su ka yi a Uyo babban birnin Akwa Ibom, gwamnonin na PDP sun nuna fushin yadda kamfanin NNPC ya zama babban kandamin a sha a yi wanka, wanda gwamnatin APC ke kamfatar maƙudan kuɗaɗe kai-tsaye ba tare da bin tsarin federaliyya wanda dokar Najeriya ta gindaya ba.
Sun kuma bayyana cewa tuni Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tashi daga bankin ‘yan Najeriya, ya koma rumbun watandar jami’an gwamnatin Buhari.
Sauran hukumomin da Gwamnonin PDP su ka zarga ana amfani da su a ƙarƙashin gwamnantin APC ana nuna bambanci da son rai ana talauta ‘yan Najeriya, sun haɗa da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA), NIMASA, NCC, Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS) da kuma Hukumar Kwastan ta Ƙasa
Sun bada misali da yadda NNPC ke kashe kuɗaɗen fetur duk yadda ta ga dama, a lokacin da ta ga dama, ga wanda ta ga dama kuma ko nawa ta ga dama.
Gwamnonin sun tunatar yadda watan Afrilu NNPC ya ƙi bai wa Gwamnatin Najeriya ko sisi daga kuɗaɗen da ya kamata ta bayar daga cinikin fetur, domin a raba wa Tarayya, Ƙananan Hukumomi da Jihohi.
Wannan mummunan hukuncin karya doka inji PDP, ya tauye wa ‘yan Najeriya kuɗaɗen da suka kamata a yi masu ayyukan bunƙasa ƙasa.
CBN Ya Zama ‘Yar-rototuwar Da Ke Wa Gwamnatin APC Aman Kuɗi Su Na Lashewa -Gwamnonin PDP
“Shi kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zama ‘yar-rototuwar da ke wa gwamnatin APC aman kuɗi su na lashewa a lokacin da su ke so.
“CBN ya zama babu mai sa masa ido ko mai hana bankin duk abin da ya ga damar yi. Domin ta kai har ya na buga kuɗaɗe yadda ya ga dama, ya yi abin da ya ga dama da kuɗaɗen kuma ya kashe duk abin da ya ke son kashewa, ba tare da ana yi masa linzami ba.”
A ƙarshe gwamnonin waɗanda a taron, har da Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto, sun yi kira ga bankunan Najeriya da su taimaka su ceto naira daga karyewar da darajar ta ke yi a dullum wayewar gari.