ZAMFARA: Matawalle ya buɗe kasuwannin mako-mako da wasu manyan kantina

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya sanar da buɗe kasuwannin mako-mako da aka rufe saboda matsalar tsaro da ya addabi jihar.

Manyan shaguna kamar su Lalan ;Garejin Mailena ; da Yar Hanya, za. Abuɗe su amma bisa wasu sharuɗɗa kamar haka:

Ba za su rika bari manyan motoci na yada zango a nan ba. Idan mota ta zo ta yi abinda ya kawo ta ta kara gaba.

Haka kuma suma ba za su rika wuce karfe 8 na dare a buɗe ba.

Sannakuma akwai mahaɗa da aka buɗe da suka haɗa da Badarawa – Jangebe, Colony; Shinkafi – Zurmi junction; da Tushar Maduwa, Shinkafi.

Kasuwanni da aka buɗe sun haɗa da:
Kasuwar Anka; Bagega Kara; kasuwar Bakura; Kasuwar Birnin Magaji; Nasarawa Burkullu Kara; Bungudu Kara; kasuwar Wanke da Kara; kasuwar Magami da Kara; kasuwar Mada da Kara;kasuwar Kauran Namoda da Kara; Kasuwar Kurya; kasuwar Kaya Maradun; Faru; Dansadau Kara; Mayanchi da Kara; Jangebe da Kara;Dauran da Kara; da kuma kasuwar Moriki da Kara.

Ka karshe gwamna Matawalle ya ce umarce askarawa da zasu rika sa ido domin tabbatar da an bi wannan doka sau da kafa.

Har yanzu jihar Zamfara bata yi sallama da matsalar tsaro ba kamar yadda sauran jihohin dake fama da matsalar a yankin arewa maso yamma ke fama da shi.