BABBAN MAGANA: Gwamnonin Najeriya kaf dinsu 36 za su yi ganawar gaggawa a Abuja

Babban Darektan kungiyar gwamnoninin Najeriya NGF
Asishana Okauru ba fidda sanarwar ganawar gaggawa na duka gwamnonin Najeriya 36 a Abuja

Wannan shine karon farko da za a yi taro ba ta yanar gizo ba.

Kamar yadda sanarwar ta ce, za a yi taron a Hedikwatar NGF ɗin ranar Laraba 19 ga wata.

” Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, gwamnan Ekiri, Kayode Fayemina gayyatar duka gwamnonin ƙasarnan domin yin ganawar musamman don tattauna wasu muhimman batutuwa da suka taso.

Kakakin kungiyar, Abdulrazaque Bello-Barkindo ya ce tuni har an aika wa gwamnonin da takardar gayyatar.

” Za a fara ganawar tun daga karfe 8 na safe ranar Laraba sannan kuma bayan haka gwamnonin za su amsa tambayoyi daga manema labarai bayan haka.