Miji ya roƙi kotu ta raba auren su, ya ce matar sa na ‘shigar-tsiraici, kai kwartaye cikin ɗakin ta da yi wa kwastomomi wawan-zama’

A ranar Juma’a ce wani mutum mai suna Oluwaniyi Olajire ya roƙi Kotun Ƙararrakin Al’adun Gargajiya ta Ibadan ta tsinke igiyar auren sa da matar sa mai suna Olabake, bisa zargin ta na neman maza da shigar fidda tsiraici a waje.

Olajire wanda mazaunin unguwar Onikoro-Akoro ne a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ya ce matar sa na na shagon sayar da abinci, inda ya ce ƙarti na zuwa da kwastomomi ta na yi masu wawan-zama, kuma ta na sa matsatstsun kaya masu fitar da surar jikin ta, don kawai ta ja hankalin maza.

Olajire bai tsaya a nan ba, ya ƙara shaida wa kotun cewa har garsaƙa-garsaƙan ƙarti matar sa ke kai wa cikin gidan sa, har cikin ɗakin ta.

“Na kasance na riƙe ta da mutunci tun da muka yi aure cikin 2010, ban bar ta da yunwa ko ƙishirwa ba.

“Amma ba ta daɗe da tarewa ba, sai ta daina yin shigar mutunci, ta riƙa saka ɗamammun kaya ta na zuwa da su wurin da ta ke sayar da abinci, ta na jan hankalin maza.

“Akwai ma ranar da mu ka yi faɗa kaca-kaca saboda na yi mata magana kan wani mutum da na tabbatar cewa farkan ta ne. Har kulle ni sai da ta sa ‘yan sanda su ka yi, a kan farkan na ta.”

Daga nan Olajire ya damƙa wa kotu wani hoton ta da aka ɗauka a ɓoye, a lokacin da ta isa wani otal, domin zuwa aikata fasiƙanci da wani kwarton ta.

Matar ba ta musanta zargin da mijin ta ya yi mata ba.

Sai dai ta ce duk shi ne ya janyo, domin ba ya ciyar da ita da ‘ya’yan su uku.

“Hatta abincin da na ke sayarwa ma ni ce na ƙuƙuta na tara jari na.” Inji ta.

Tun da farko mijin ya shaida wa kotu cewa ta kwashe ‘yan su uku, waɗanda ya ce a yanzu bai san inda su ke ba.

Kan wannan ne Mai Shari’a ya umarce ta da ta kawo yaran kotu, kuma ya ja layi, ya ce kada wanda ya tsokani wani tsakanin su.

Ya ce a koma kotu ranar 3 Ga Maris, domin ya yanke hukunci.