ZAMFARA BA SAUƘI: ‘Yan bindiga sun arce da dagaci, matar sa da mutum 11 a yankin Maru

Kwanaki bakwai bayan ‘yan bindiga sun ƙone ƙauyuka biyu ƙurmus, kuma su ka kashe mutum 200 a Jihar Zamfara, a ranar Litinin kuma sun kai wa ƙauyen ‘Yarkuka hari, inda su ka arce da Dagacin ‘Yarkuka Sarki Musa, matar sa Hadiza Musa da kuma wani ƙanin sa.

Ba a nan su ka tsaya ba, maharan sun yi gaba da wasu ‘yan ƙasar Burkina Faso biyu, waɗanda ke aikin haƙar ma’adainai a cikin Ƙaramar Hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Hare-haren guda biyu ne sauka kai a yankin, domin sun shiga ƙauyen Kadauri suka saci matan aure uku da ‘yan mata biyu masu ƙananan shekaru.

Rahoton da wakilin mu ya samu daga ‘Yarkuka ya nuna cewa maharan sun dira ƙauyen wajen 2:30 na rana. Ba su harbi kowa ba, amma sun darkaki gidan dagacin garin kai-tsaye, su ka ta kama shi da matar sa da kuma wani ƙanin sa.

Wanda aka arce da matan sa biyu a ƙauyen ‘Yarkuka mai suna Mohammed Tasiu, ya shaida wa Premium Times cewa a gaban sa aka tafi da matan sa biyu da kuma ‘yan mata uku.

“Sun shigo tsakar dare sun tafi da mata na biyu, Zainab da Asma’u. Tun da mu ka yi magana da su sau ɗaya, ba mu ƙara jin ɗuriyar su ba.” Inji Tasiu.

PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Zamfara, Mohammed Shehu, amma ya ce bai samu labarin wannan mummunan lamari ba.