KIBIYAR AJALI: Yadda shekarar 2022 ta fara da ɗaukar rayukan manya a Najeriya

Yayin da shekarar 2020 ta tafi da rayukan wasu manyan Najeriya, cikin har da makusantan Shugaba Muhammadu Buhari guda uku, wato Abba Kyari, Sama’ila Mamman da Sam Nda-Isaiah, shekarar 2022 ma ta fara da ɗaukar rayukan manyan ‘yan siyasa da wasu mashahurai a ƙasar nan.

Farkon shekarar ce aka tashi da rasuwar babban Basaraken Ibadan, Olubadan Saliu Adetunji, wanda ya hau sarauta cikin 2016.

Kwana biyu kuma aka tashi da rasuwar dattajo Bashir Tofa a Kano. Mutuwar Tofa ta jefa Arewa cikin damuwa, musamman ganin da ake masa irin burbushin sauran dattawan da ke faɗa-a-ji a Arewa.

Bashir Tofa bai cika mako ɗaya da rasuwa ba, sai mutuwa ta ratsa cikin manyan malaman Musulunci a Najeriya, ta ɗauki ran Dakta Ahmad, malamin da ya shafe sama da shekaru 30 ya na karantar da Hadisai a Kano.

Mako ɗaya bayan rasuwar babban Shehin malamin, sai mutuwa ta ɗauki tsohon Shugaban Riƙon Ƙwayar mulkin Najeriya, Earnest Shonekan, a ranar Talata.

Washegarin mutuwar Shonekan ne kuma a ranar Laraba aka wayi gari da labarin rasuwar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Adetunji Alao-Akala.

Alao Akala wanda ya yi mulki tsakanin 2007 zuwa 2011 a ƙarƙashin PDP, ya rasu a cikin ɗakin sa, a Ogbomoso, garin sa na haihuwa.

Sanarwar da Kakakin APC Olafunde Abdul’aziz ya fitar, ya ce Ladoja ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Kafin ya zama gwamnan Oyo, Ladoja ya zama mataimakin Rashidi Ladoja tsakanin 2003 zuwa 2006.

Bayan tsige Ladoja ne sai Alao Akala ya zama Gwamnan Riƙo. Ya tsaya takara a 2007 ya ci ƙarƙashin PDP.