AFCON: Alƙalin wasa ya birkice a wasan Mali da Tunisia, ya hura tashin sau biyu lokaci bai cika ba

Alƙalin wasan da ya hura wasa tsakanin Mali da Tunisia ya birkice, ya ruɗe, inda ya hura tashi ana minti 85. Bayan an ankarar da shi kuma sai aka koma a ka ci gaba da wasa,

Bayan minti hudu kuma sai ya sake hura tashi wato saura minti 1 a gama wasan.

Wannan alkalin wasa dai ya birkice inda wasan ta kusa kwace masa. Ya baiwa Tunisia bugun daga kai sai gola, amma duk da cewa ba hakan ya hura wa usur ba.

Haka kuma ya danna wa wani ɗan wasan Mali jan kati a laifin da ake ganin bai cancanci jan kati ba.

Kasar Tunisia sun harzuka inda suka rika kai ƙara wa alkalan bayan fage suna korafin an cuce su.

Masu sharhi sun ce akwai sake domin wannan alkalin wasa ya tuzarta wasan cin kofin Afrika ne da ake yi a Kamaru.

” Akwai yiwuwar ba za a sake saka shi ya hura wasa a wannan gasa ba. Saboda, bayan sau biyu yana hura a je a huta na mintina 5, sannan ga bata lokaci da aka yi na canje-canjen ƴan wasa da kuma na laifuka da aka hura har da na bugun daga kai sai gola sau biyu, duk bai sa ya kara lokaci ba sai dai ma ragewa da yayi.” In ji Okocha.