Alkalin Wasa Zai Sanya Kyamara A Goshinsa A Fafatawar Crystal Palace Da Manchester United

Alkalin wasa Jarred Gillett zai daura kyamara a goshinsa a yayin fafatawar gasar firimiya da za’a yi a yau Litinin tsakanin Crystal Palace da Manchester United, a cewar hukumomin shirya gasar.