ZALUNCI KO MUGUNTA: Yadda saurayi ya shake budurwarsa sai da ta mutu saboda ta ki zubar da cikin da yayi mata a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta tsinci gawar wata budurwa a gefan titi a kauyen Anadariya dake karamar hukumar Bebeji jihar Kano da aka kashe.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa ‘yan sanda sun tsinci gawar ne ranar 26 ga watan Maris bayan kirar su da aka yi zuwa wurin da misalin karfe 8 na yamma.
Kiyawa ya ce bisa ga umarnin kwamishinan ‘yan sandan jihar Mamman Dauda ‘yan sandan su kai gawar zuwa babban asibitin Tirga inda likitoci suka tabbatar cewa ta rasu.
Ya ce binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa sunan budurwar Teresa Yakubu sannan an kashe ta ne ta hanyar shake ta da dankwalinta.
Kiyawa ya ce binciken ya kuma nuna cewa saurayin marigayiyan wani mai suna Phillipbus Ibrahim mai shekara 20 Kuma mazaunin Unguwar Korau a karamar hukumar Tudun-Wada ne ya aikata wannan ta’asa tare da taimakon abokinsa Gabriel Bilal mai shekara 25 mazaunin Unguwar Korau karamar hukumar Tudun-Wada Kano.
A hannun jami’an tsaro Ibrahim ya ce ya kashe budurwarsa saboda yadda ta ki amincewa a zubar da cikin da yayi mata na wata biyu.
Ibrahim ya ce Teresa mazauniyar Nasarawa ce a karamar hukumar Bebeji. Yace a ranar Litini da yamma ya dauke ta ya kai ta wani wuri ya kashe ta tare da taimakon abokin sa Gabriel saboda ta ki yarda ta zubar da cikin da yayi mata.
“Da farko dai mun bata wani magani ta sha domin cikin ya zube amma bai yi aiki ba sai dai ta rika cewa cikin ta na mata ciwo ne kawai. Daga nan ne da ni da abokina Bilal muka dauke ta a babur zuwa Wani wuri inda a nan ne ni na shake ta da galen ta sannan shi Bilal ya rike hanna yenta da kafafuwanta, nan dai ta rika shure-shure.
Ibrahim ya ce a lokacin da suka bar wurin akwai alamun da saurar numfashi a jikinta amma ta galabaita.
Abokin Ibrahim, Bilal ya yi nadamar abin da ya aikata tare da abokinsa inda yake cewa ya aikata haka ne ganin cewa Ibrahim abokinsa ne na kud-da-kud.
A ƙarshe Kiyawa ya ce da zarar rundunar ta kammala bincike za ta kai wadannan mutane kotu domin a yi musu hukunci.