SHARI’AR MAKWABTA DA ZAKARA A KANO: Makwabta sun yi nasara, an umarci Shu’aibu ya yanka zakarar

Kotun majistare dake Gidan Murtala a jihar Kano ta umarci wani Isyaku Shu’aibu da ya yanka zakaransa saboda cara da yake yawan yi har yana hana makwabta barci.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan karar da wasu makwabtan Shu’aibu su biyu suka kawo gabanta ta.
Wani makwabcin Shu’aibu, Yusuf Muhammed dake zama a kwatas din Ja’en a cikin garin Kano ya bayyana a kotun yadda carar zakarar Shu’aibu ke hana shi barci da sukuni a gidansa.
Shu’aibu bayan ya amince da laifin zakararsa ya roki kotun da ta dage shari’a har zuwa Juma’a.
A ranar Juma’a alkalin kotun Halima Wali ta yanke hukuncin cewa lallai Shu’aibu ya killace zakarar sa sannan ya yanka shi domin hakkin makwabtaka da ya shiga.