Yadda ƴan bindiga suka yi garkuwa da dalibai 10 na makarantar Sakandare a Kachia, Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ta samu rahoto daga jami’an tsaro cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai 10 a makarantar sakandare dake karamar hukumar Kachia.
Kwamishinan tsaron jihar Samuel Aruwan ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai ranar Talata a garin Kaduna.
Aruwan ya ce maharan sun yi garkuwa da daliban makarantar sakandare Awon ranar Litini da safe.
Ya ce zuwa yanzu babu wanda ke da masaniyar inda masu garkuwan suka arce da waɗannan yara sai dai jami’an taso sun fantsama farautar su don su ceto yaran sannan su yi dagadaga da yan bindigan.
Idan ba a manta ba gwamnatin Kaduna ta saka dokar hana walwala na awa 24 a unguwannin Nasarawa da Tirkaniya dake karkashin karamar hukumar Chikun bayan kashe wasu mutum biyu da a kayi a dalilin rikishin yan kwaya.
Gwamnatin ta saka dokar hana walwalar ne domin hana barkewar rikici a yankin.
Aruwan wanda ya sanar da haka ya ce gwamnati ta yanke wannan hukunci ne bayan ta tattauna da jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda da SSS sannan da shugabannin gargajiya dake unguwan Sabon Gari.
Ya ce dokar ya hada da hana bukukuwan Kidan Bishi, Kidan Gala da yawon farauta da mutane ke yi a yankin.