ZAƁEN 2023: Banda ruwan-ido, zaɓen-tumun-dare, mu tsaida ɗan takarar da duk zai iya yi wa APC dukan-kabarin-kishiya – Nasihar Gwamna Wike ga na Oyo

Gwamnan Jihar Ribas Nysom Wike ya ja kunnen dukkan gwamnonin PDP cewa su haɗa kai su goyi bayan ɗan takarar da PDP ta tsayar a zaɓen 2023 domin a kawar da jam’iyyar APC a kan mulki.

Wike ya yi wannan gargaɗi ne yayin da ya kai wa Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ziyarar neman haɗin kan gwamnonin PDP baki ɗaya, domin su tabbatar da samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa.

“Idan mu ka haɗa kan mu, to ina tabbatar da cewa za su iya kawar da APC ba tare da ɓata lokaci ba. Amma idan mu ka kasa kawar da APC, to ‘yan Najeriya za su ji haushin mu sosai.” Inji Wike.

Wike ya kai ziyarar ce a Fadar Gwamnatin Jihar Oyo tare da rakiyar tsohon Gwamna Clestine Omehia da wasu ‘yan Majalisar Tarayya biyu.

Sannan kuma akwai tsohon Mashawarcin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan a kan Harkokin Afuwa Ga ‘Yan Neja-Delta, Timi Alaibe. Akwai kuka tsohon Ministan Harkokin Sufuri, Abiye Sekibo da sauran su.

“Kada a damu da wanda za tsayar takara, muddin dai zai iya kayar da APC, to shi ne buƙatar mu. Kada mu tsaya ruwan-ido ko biye wa son-zuciya. In dai wanda zai iya yi wa APC dukan-kabarin-kishiya, to hakan mu ke so.

Wike da tawagar sa sun kuma je Fadar Olubadan na Ibadan, inda su ka yi ta’aziyyar rasuwar Olubadan Saliu Adetunji.

Sannan kuma ya yaba wa ƙoƙarin da Gwamna Makinde ya yi a matsayin sa na Sakataren Tsare-tsaren Taron Gangamin PDP, wanda aka zaɓi Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyya. Ya ce ashe Makinde babban jarimi ne sosai.