‘Yan sanda sun kama mutumin da ya kashe mijin farkarsa a Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa ta kama Abdullahi Sale mai shekara 22 da ake zargin ya kashe mijin farkarsa da adda.

Sale ya sare mijin farkarsa Muhammad Tukur mai shekara 22 da adda ranar 7 ga Janairu a kauyen Rabadan dake karamar hukumar Birnin Kudu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Lawan Adam wanda ya sanar da haka a wata takarda da manema labarai suka samu ya ce Tukur ya gamu da ajalinsa bayan ya tafi yi wa Sale gargadin ya rabu da matarsa.

“A wannan rana Tukur ya suntumi addar ya garzaya gidan Sale inda garin ya ja masa kunne da gargadi game da matarsa da ya ke bibiya sai cacanbaki ya barke a tsakanin su. Daga nan sai Sale ya fizge addar daka hannu Tukur ya sassare shi, ya mummunar raunin a jikinsa.

Adam ya ce Tukur ya rasu a asibitin FMC dake Birnin Kudu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sale Tafida ya ce fannin dake gurfanar da masu aikata laifi irin na jihar dake Dutse za ta ci gaba da gudanar da bincike.

Idan ba a manta ba a ranar Litini din wannan mako PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ‘yan sandan jihar Jigawa dai ke farautar wani matashi mai shekara 22 da ya kashe wansa da wuka.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Lawan Shiisu ya ce wannan abin tashin hankalin ya faru ranar 5 ga Janairu a kauyen Sabuwa Takur dake karamar hukumar Dutse.

Shiisu ya ce Alfred Julius mai shekara 22, ya kashe wansa Augustine Julius mai shekara 30 da wuka bayan sun samu rashin jituwa a tsakanin su.

Ya ce Alfred ya gudu sannan Augustine ya rasu yayin da likitoci ke duba shi.

Shiisu ya ce tare da hadin gwiwar iyalin Ochai rundunar ta fara farautar Alfred domin yanke masa hukunci bisa laifin da ya aikata.