‘Zaɓen 2023 bai yi ingancin da aka so ya yi ba’ – Adamu, Shugaban APC

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu, ya amince da cewa zaɓen ranar 25 ga Fabrairu bai cikakkiyar nagartar da aka so ya yi ba.
Adamu ya bayyana haka ne a ranar Litinin, lokacin da ya ke jawabi a taron ganawar da Shugabannin APC su ka yi da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, mataimakin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Kashim Shettima da kuma sanatoci da ‘yan majalisar tarayya da su ka yi nasara a ƙarƙashin APC.
Sun yi ganawar ce ta sirri a babban ɗakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa, a Abuja,a ranar Litinin.
Sai dai kuma Adamu ya ce duk da ƙalubalen da aka fuskata, APC ce dai ta yi nasara ƙarara.
Da ya ke magana kan cikas ɗin da aka ci karo da shi yayin zaɓen, ya ce shi fa ya na ganin ba za a iya samun sahihin zaɓe ba.
Duk da haka Adamu ya taya waɗanda su ka yi nasara murna, tare da jinjina masu. “Daga ranar 29 Ga Mayu, nauyin haɗa kan Najeriya, samar da zaman lafiya da ci gaban ƙasar nan zai rataya a wuyan ku.” Inji shi.
Sai dai kuma ra’ayin Adamu ya sha bamban da na Fadar Shugaban Ƙasa, wanda ita fadar ta bayyana cewa ba a taɓa gudanar da zaɓe wanda ya kai kyan na 2023 ba.
Fadar ta fitar da sanarwa cewa, “zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya fi zaɓukan baya inganci.”
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya samu ci gaba sosai fiye da zaɓukan baya da aka gudanar.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya aika wa PREMIUM TIMES a ranar Litinin.
“An samu ci gaba sosai a wannan zaɓen na shugaban ƙasa, idan aka kwatanta da zaɓukan da aka yi a baya. Wannan kuwa ƙoƙari ne da jajircewar da wannan gwamnati ta yi, tare kuma da jajircewar ‘yan Najeriya. Su ne su ka cancanci a yi masu jinjina,” inji Shehu.
A cikin sanarwar ta Shehu, Fadar Shugaban Ƙasa ta gode wa tsoffin jakadu Mark Green da Johnnie Carson, tare da sauran masu sa-ido kan zaɓe na ƙasashe daban-daban, waɗanda su ka nuna damuwa dangane da zaɓen Najeriya da kuma rawar da su ka taka ta masu sa-ido.
“Sai dai kuma babu wanda ya ke jayayya da sakamakon zaɓen na shugaban ƙasa, sai fa waɗanda ba su yi nasara ba kaɗai.
“Zaɓen shugaban ƙasa wanda aka fi yin gwagwagwar takara a tarihin Najeriya, shi ne wannan na 2023, kuma mutum ɗaya ne ya yi nasara, Bola Tinubu.
“Amirka da Shugaban Birtaniya duk sun taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasa murnar lashe zaɓe da ya yi. Haka yawancin ƙasashen ECOWAS da na sauran yankunan Afrika.
“Tabbas an ɗan samu matsalolin fara zaɓe kan lokaci da kuma cikas na lattin isar malaman zaɓe da wuri. Wannan kuwa ba sabon abu ba ne ko a baya, kuma ko a sauran ƙasashen duniya, irin hakan kan faru.”
Shehu ya ce sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da kuma nasarar da APC ta samu a zaɓen Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa ya nuna a ƙasa baki ɗaya ‘yan Najeriya sun ƙara tabbatar wa kan su da duniya cewa a ƙasar nan dai har yau babu kamar jam’iyyar APC. Wannan gamsuwa da amanna da suka yi da jam’iyyar ce Garba Shehu ya ce ta sa suka sake zaɓen ta a karo na uku a jere.