Ba mu wani nuƙu-nuƙu, duk wanda kotu ta umarci INEC ta ba shi bayanan zaɓe, za mu bayar – Yakubu

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa a shirye ta ke ta damƙa kwafen bayanai da dukkan kayan da kotu ta bayar da umarni ga jam’iyyu ko ‘yan takarar da ke ƙorafi kan zaɓen ranar 25 ga Fabrairu, domin su yi nazarin da su ke so su yi.
Shugaban hukumar ne, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, lokacin da ya karɓi tawagar lauyoyin jam’iyyar LP bisa jagorancin Babban Lauya Livy Uzoukwu.
Tawagar ta lauyoyin na LP dai sun ziyarci Hedikwatar INEC ce a ranar Litinin, a Abuja.
Yakubu ya tabbatar masu da cewa ya karɓi wasiƙar da LP ta aika masa a ranar 6 ga Maris, wadda ta sanar da shi cewa waɗannan lauyoyi za su kai ziyara INEC domin duba kayan zaɓe.
Ya ce wasiƙar na ɗauke da ƙarin bayanin sanar da shi cewa ya sanar da Kwamishinonin Zaɓe na INEC da ke a kowace jiha, cikin jihohi 36 na faɗin ƙasar nan da FCT Abuja.
Wasiƙar dai ta nemi INEC ta umarci Kwamishinonin Zaɓe na jihohin su damƙa wa LP bayanai da kayan da ta ke buƙata domin gabatar da bayanan ƙarar ta a kotu.
Yakubu ya ce INEC ta shirya shirya gudanar da taro da Kwamishinonin Zaɓe, domin su tattauna batutuwa da dama, ciki har da batun bayar da sahihan kwafe-kwafe na bayanan zaɓe ga dukkan waɗanda su ka shigar da ƙara, ba ma ga LP ita kaɗai ba.
“Ina tabbatar maku da cewa INEC ba ta wani nuƙu-nuƙun ɓoye komai. Za mu ba ku dukkan abin da ku ke buƙata.
“Kwafen bayanai biyu ne ke a hannun Hedikwatar INEC nan a Abuja. Kuma za mu iya samar maku waɗannan kwafen ba tare da ɓata lokacin. Akwai EC8Ds da aka tattara daga jihohi da kuma mai lamba EC8DA, wanda sakamakon zaɓe ne da INEC da kan ta ta tattaro daga cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.
“Mai lamba EC8DA dai ina jin kwafe 39 ne. Kuma za mu iya samar maku kwafen su ba tare da ɓata lokaci ba,” inji Yakubu.
Ya ce sauran kwafen bayanai kuma duk su na ofisoshin INEC na jihohi daban-daban, kuma hukumar za ta so sanin ranakun da lauyoyin za su je jihohi domin a shirya masu kwafen kafin su isa, yadda su na zuwa sai dai su fara nazari kawai’.
“Sauran bayanai kuma alƙaluma ne lambobi da bayanan tantance mai shaidar katin rajistar zaɓe na rumfunan zaɓe fiye da 176,000.
“Za mu samu lokaci mu buga kwafe-kwafen su a wadace, sannan mu damƙa maku cikin hanzari.”
Daga nan ya shawarci tawagar lauyoyin INEC su gana da lauyoyin INEC domin su bayyana wa juna batutuwa da dama.
Jagoran tawagar lauyoyin LP, Uzoukwu ya shaida wa Yakubu cewa dalilin ziyarar shi ne domin su share hanyar fara nazarin kayan zaɓen shugaban ƙasa. “Saboda ka san dai mu na da kwanaki 21, waɗanda a cikin su ne za mu shigar da ƙara, a madadin waɗanda mu ke karewa. Yanzu kuma daga cikin kwanaki 21 ɗin, kusan kwanaki 10 kaɗai ne su ka rage mana. Ga shi kuma har yau ɗin nan ba mu karɓi kwafen takardun bayanai ko kayan zaɓe ko da guda ɗaya ba.”