Yadda wasu ‘yan Najeriya 3 suka makale a kafadar jirgin ruwa tun daga Legas har kasar Spain

An gano wasu ‘yan Najeriya uku da suka boye a kafadar jirgin ruwan da ya yi tafiyar kwanaki 11 daga Najeriya zuwa Canary Islands dake kasar Spain.
Kamfanin Dillancin Labaran kasar Spain EFE ta ce likitoci ne suka gano wadannan mutane makale a kafadar jirgin a tashar jiragen ruwa inda suka kai su asibiti a Gran Canaria domin a duba su.
An sallami mutum biyu amma daya na kwance a asibitin kuma yana samun sauki.
Sai dai har yanzu babu tabbacin ko wadannan mutane sun makale a kafadar jirgin ne tun daga Najeriya har tsibirin Canary Islands.
Mashawarcin shiga da fita na tsibirin Canary Islands Txema Santana ya ce tun da jirgin ta tashi daga Najeriya ba ta tsaya a ko ina ba sai da ta isa wannan tsibiri.
Santana ya ce ‘yan Najeriyan sun bayyana cewa su ne kadai suka isa kasar Spain da ransu wanda hakan ke nuna cewa akwai yiwuwar suna da yawa da suka boye a kafadar jirgin a tsawon wannan tafiya.