ALAMOMIN ƘARSHEN WA’ADIN MULKI: Gwamnatin Tarayya ta ce gwamnoni ne su ka ƙaƙaba wa jama’a talauci da ƙuncin rayuwa a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ɗora laifin ƙaruwar fatara, talauci da ƙuncin rayuwar da ‘yan Najeriya ke fuskanta a kan gwamnonin jihohi.
Ƙaramin Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Clement Agba ne ya ce wannan ƙuncin rayuwa da ake fuskanta a faɗin ƙasar nan, gwamnonin jihohi ne su ka haifar da shi, ta hanyar kashe maƙudan kuɗaɗe wajen yin ayyukan da ba su da wani tasiri wajen inganta rayuwar al’umma.
Agba ya yi wannan kakkausan ikirarin ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa a Aso Rock Villa, Abuja, ranar Laraba.
Agba ya ce gwamnoni sun riƙa yin bindiga da maƙudan kuɗaɗe wajen gina gadoji da filayen jiragen sama, waɗanda ba su da wani tasiri a wajen inganta rayuwar al’umma, musamman na karkara.
Minista Agba ya ce kashi 72 cikin 100 na matalauta duk a yankunan karkara su ke. “Amma gwamnoni sun yi watsi da su, su ka maida hankali wajen gine-gine da gadoji a cikin manyan biranen jihohin su.”
“Shi ya sa ba za ka taɓa ganin wani aikin raya karkara ba, saboda a cikin babban birnin jiha kaɗai za ka ga ana aiki. Ita kuwa dimokraɗiyya aiki ne na kai gagarimin ayyukan raya ƙasa cikin mutane masu tarin yawa. Mu kuwa akasarin al’ummar mu duk a yankunan karkara su ke,” inji Minista Agba.
“Gwamnatin Tarayya na bakin na ta ƙoƙarin. To ni dai ina ganin maimakon gwamnoni su riƙa ciwo bashi su na gina filayen jiragen sama, alhali akwai wasu filayen a maƙwautan jihohin su, ko su riƙa gina gadojin sama, to kamata ya yi su maida hankula wajen gina titina a yankunan karkara, yadda talakawa za su samu sauƙin kai amfanin gonar su kasuwa don su sayar su biya buƙatun su na yau da kullum.”
‘Gwamnoni Da Ciyamomi Su Ka Jefa Mutanen Karkara Cikin Masifa’ – Buhari:
Shi ma Shugaba Muhammadu Buhari, ya jaddada cewa Gwamnoni da ciyamomi ne gaggan ‘yan rashawa a Ƙananan Hukumomi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ragargaji yadda gwamnoni da ciyamomin ƙananan hukumomi ke ɗaure wa rashawa da cin hanci gindi, lamarin da ya ce su ne ke hana samar da ci-gaba a yankunan karkara.
Buhari ya yi wannan kakkausar suka a lokacin da ya ke jawabi wurin taron Manyan Jami’ai na 44 (2022), a Cibiyar Nazarin Tsare-tsaren Mulki, Kuru, a Abuja, ranar Alhamis.
Buhari ya bada labarin irin gaganiyar da ya sha wajen daƙile cin hanci da rashawa.
Ya bada labarin irin gaganiyar da ya riƙa sha da wasu gwamnoni dangane da yadda su ke riƙon ƙananan hukumomin su.
“Ina ganin ya zama dole na ɗan saki layi daga abin da na ke bayani a kai, tunda na gama jawabi na. Abin da zan bada labari kuwa, ni ganau ne, ba jiyau ba.
“Wato irin harƙallar da su ke yi, idan misali kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya za ta bai wa wata jiha naira miliyan 100 ne za a bai wa ƙaramar hukuma, sai jiha ta ba shi naira miliyan 50, amma zai sa hannu cewa naira miliyan 100 ya karɓa.
“Sauran Naira miliyan 50 kuwa sai gwamna ya sa aljihu, sai fa wanda ya ga dama zai bai wa ladar-ganin-ido.
“Shi kuma shugaban ƙaramar hukuma, sauran kuɗaɗe ko biyan albashi ba za su ishe shi ba. Daga nan sai ya yi watsi da ayyukan raya karkara, da ya biya kan sa da wasu manya ‘yan ƙalilan, sauran shi ma sai ya watsa cikin aljihun sa.
“To abin da ke faruwa kenan yanzu a Najeriya. Lamarin ya yi muni matuƙa. Kuma abin takaici, masu ilmi ne ke yin wannan ha’inci.” Inji Buhari.
Daga nan Buhari ya ja kunnen ma’aikatan gwamnati da sauran masu riƙa da muƙamai su riƙa aiki tsakani da Allah.