Yadda muka damke Nnamdi Kanu daga ƙasashen waje muka maido shi Najeriya – Malami

Ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta haɗa hannu ne da jami’an tsaro na sirri a kasashen waje sikq kamo Nnamdi Kanu.

Malami ya ce tuni har an dawo da shi kasa Najeriya domin ci gaba da fuskantar shari’a.

Dama kuma Kanu ya waske ke ne akan neme shi aka rasa bayan bashi beli da kotu tayi.

Tun daga lokacin ake ta neman sa, ba ayi nasarar kama shi ba sai yanzu.

A jawabi da Malami yayi da ƴan jarida a Abuja, ya ce Kanu zai ci gaba da bayyana a gaban kotu, sannan ba za ayi sakacin sake bari ya yi layar zana ba.

Tun bayan guduwar sa kasar Isra’ila inda nan ne aka fi ganin sa, mabiyan sa ƴan ƙabilar Inyamirai suka rika kai hare-hare a yankunan su.

Kungiyar IPOB wanda ita ce kungiyar sa yake shugabanta ta kafa bangaren mayaka da suka yi wa suna ESN.

Wannan kungiya basu bar kowa ba musamman idan kana ɗan Arewa.

Baya ga gallaza wa mutanen su azaba da suke yi su kan bi rugagen Fulani suna babbakewa sannan su kashe na kashewa.

Sai dai daga baya bayan nan basu ji da daɗi ba domin jami’an tsaro sun rika fatattakarsu suna kashe su saboda azabar da suke gallaza wa mutane.

Malami ya ce hukumomin Najeriya sun haɗa hannu da na kasashen waje, suka damke shi.