Dalilin da ya sa aka daina kashe wa Hukumar Yaƙi da Rashawar Kano kuɗi -Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana raddi ga kalaman Shugaban Hukumar Hana Rashawa da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji, wanda ya ce gwamnatin ta daina kashe wa hukumar kuɗi shi ya sa ya ɗauƙi ƙoƙo ya ke bara.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ya shaida wa BBC Hausa cewa matsalar rashin kuɗi da Gwamnatin Jihar Kano ke fama da ita ce ta sa gwamnantin ta daina kula da buƙatun hukumar na gaggawa da na wajibi.

Garba ya ce hukumomi da yawa da ke ƙarƙashin gwamnantin ta Kano abin ya shafa, ba hukumar da Muhuyi ke shugabanci ba.

Amma kuma ya ce duk da haka Gwamnatin Jihar Kano na bai wa hukumar duk wani goyon bayan da ta ke bukata.

Sannan kuma Garba ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa gwamnati na ƙoƙarin tsige Muhuyi daga shugabancin hukumar.

“Ita fa gwamnati za ta iya cire duk wani ma’aikacin ta, ba tare da an riƙa yayatawa, muddin buƙatar cire shi ɗin ta taso.” Inji Garba.

An kasa samun Magaji a ranar Talata, domin a ji ko gaskiya ne idan ya na binciken wata harƙalla, daƙasharama da wuru-wurun kwangilar bilyoyin kuɗaɗen da ake ganin dalilin binciken ne shi da hukumar sa su ka shiga halin ƙuncin da su ka samu kan su a yanzu.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Muhuyi, Shugaban Yaƙi da Rashawa na Kano ya zargi jami’an gwamnatin Kano na yi masa ‘barazana da katsalandan.’

Shugaban Hukumar Hana Rashawa da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji, ya yi ƙoƙarin cewa ya na fuskantar barazana da katsalandan’ daga jami’an gwamnati.

Yayin da Magaji bai bayyana sunayen masu yi masa katsalandan’ ɗin ba, ya ce abin da ake yi masa ba zai dakushe kaifin ƙoƙarin da ya ke yi na gurfanar da ɓarayin gwamnati a Jihar Kano ba.

Magaji ya yi wannan kalami a shafin hukumar na Facebook.

“Ƙalubale da matsin-lamba da na ke samu daga jami’an gwamnati ya yi yawa. Wasu jami’an gwamnati kallo su ke ita wannan hukuma ta gwamnati ce, don haka su a ganin su, akwai wasu abubuwan da hukumar ko da ta ga ba daidai ba ne, wai kamata ya yi wannan hukumar ta kauda kai kawai. To amma ni ba zan taɓa yi masu yadda na ke so ba, saboda ba tsoron na rasa aiki na ke yi ba.”

“Har damƙe an yi an caje ni da laifin take umarni, saboda kawai ina binciken, wani kes. Amma wannan bai sage min guyawu ba, saboda aiki na yi bakin-rai-bakin-fama.

“Ina so jami’an gwamnati su sani kuma su fahimci cewa ba kai na ne na ke yi wa aikin nan ba. Kuma ba don na azurta kai na na ke yi ba. Duk ma mai yin wannan tunanin, kan sa kawai ya ke yaudara.

“Kai ni ko a yau na bar wannan aiki a jihar Kano, dokar Najeriya ta ba mutum ‘yancin yin zama mai bincike-ƙwaƙwaf mai zaman kan sa.

“Zan iya irin wannan aiki a ko’ina a Najeriya, a matsayi na na lauya mai lasisi.” Inji shi a cikin fushi.

“Gwamnatin Kano Ba Ta Bai Wa Hukuma Ta Kuɗi”:

Saboda gwamnati ba ta bayar da kuɗaɗe ga wannan hukuma shi ya sa “na ƙaddamar da gidauniyar neman tallafin kuɗaɗe dala 100,000 ga wannan hukuma.”

Ya ce duk mai son bayar da gudummawa, ƙofa a buɗe ta ke. Amma ba zai taɓa bada kai bori ya hau ba.

PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Kwamishinan Yaɗa Labarai, Mohammed Garba, amma ba ta same shi ba.