An kama Nnamdi Kanu shugaban kungiyar Biyafra

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Ofishin Ministan shari’a ya tabbatar da kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB da ke son kafa ƙasar Biyafra.

Ministan Shari’a kuma Babban Antoni Janar Abubakar Malami ne ya tabbatar da kama Nnamdi Kanu a wajen taron manema labarai da ya ƙira a Abuja ranar Talata.

Malami ya ƙara da cewa an kama shugaban IPOB ne a ranar Lahadi kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya kan zarge-zargen da ake yi masa na neman ballewa daga Najeriya da kuma hare-haren ta’addanci.

Majiyarmu ta BBC ta ruwaito Kanu yana fuskantar zarge-zargen da suka shafi cin amanar kasa lamarin da ya sa aka gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa fafutukar da yake yi wajen ganin an kafa kasar Biafra ta hanyar IPOB.

A watan Afrilun 2017 aka bayar da belinsa bisa dalilai na rashin lafiya sai dai ya tsere zuwa ƙasar Isra’ila.