YADDA MAJALISA TA YI WA KASAFIN 2022 KACA-KACA: ‘Yan Majalisa 469 sun cusa ayyukan ‘son rai’ 6576, sun zabge ayyukan Buhari 10,733

A bisa al’adar shugabanni, lokacin da hannu a kasafin kuɗi lokaci ne na murna. To amma duk duniya ta shaida cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba ya cikin farin ciki a ranar 31 Ga Disamba, 2022, lokacin da ya sa wa Kasafin 2022 hannu a Fadar Shugaban Ƙasa.

Buhari dai ya sa hannu, kuma ya shaida ko kalaman sa sun tabbatar cewa ba da son ran sa ya sa hannun ba.

Bayan ya miƙa wa majalisa kasafin a cikin Oktoba, yayin da su ka maida masa, Buhari ya gano irin dubban cushe-cushen ayyuka da Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa suka yi a cikin kasafin.

Jimlar ‘yan majalisar su 469 dai sun cusa sabbin ayyuka guda 6576 a cikin kasafin, waɗanda ba su cikin waɗanda Buhari ya aika masu.

“Babban abin damuwar shi ne dukkan ayyukan da suka cusa, akasari ayyuka ne da suka kamata a ce jihohi ne da ƙananan hukumomi za su yi su, ba gwamnantin tarayya ba.” Inji Buhari a lokacin da ya ke jawabi.

A lokacin kuma Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila su na wurin bikin sa wa kasafin hannu.

“Wani abin damuwa kuma, ‘yan majalisa sun zaftare yawan ayyuka 10,733 da ke cikin kasafin.

Cushe-cushen da ‘yan majalisa su ka yi, ya nuna kowane ɗaya ya cusa ayyukan ‘son rai’ har guda 14 kenan, a cikin Kasafin 2022.

A shekarun baya ‘yan majalisa sun sha cewa dokar Najeriya ta ba su ikon cusa ayyukan da su ke so a yi wa jama’a.

Bayan ya sa wa Kasafin 2022 hannu, Buhari ya fallasa canje-canjen asarƙalar da Majalisa ta yi wa kasafin.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa Kasafin 2022 hannu a ranar Juma’a. Sai dai kuma a cikin jawabin sa yayin da hannun, ya bayyana wa duniya irin damuwar sa kan wasu “canje-canje masu ɗaure kai” da ‘Yan Majalisa su ka banƙara ƙofar ɗakin kasafin su ka cusa a ciki.

Cikin sanarwar da Kakakin Shugaban Ƙasa Garba Shehu ya sa wa hannu, Buhari wanda ya sa wa kasafin hannu a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, ya sa hannu ne kan kasafin naira tiriliyan 17.1, saɓanin naira tiriliyan 16.3 waɗanda ya gabatar masu a cikin Oktoba.

Majalisa ta ƙara sama da biliyan 700 a cikin kasafin na 2022.

Cikin makon jiya ne Majalisar Dattawa ta ƙara masa yawa da naira biliyan 700.

Majalisar Dattawa ta yi wa Kasafin Kuɗaɗe na 2022 ƙarin naira biliyan 700.

A yanzu kasafin ya tashi daga naira tiriliyan 16.4 ya koma naira tiriliyan 17.12.

Wannan ƙarin ya zo ne ƙasa da kwana ɗaya bayan Majalisar Tarayya ta miƙa kasafin.

Haka nan kuma Majalisar Dattawa ɗin dai ta maida cewa za a yi kasafin ne daidai da dalar Amurka 62, maimakon dala 57 da Buhari ya yi kasafin da farko.

Dalilin yin haka kuma shi ne saboda farashin gangar ɗanyen mai ta ƙaru bayan Buhari ya gabatar da kasafin a kan dala 57.

Sannan kuma an amince za a riƙa haƙo gangar ɗanyen mai miliyan 1.86 a kowace rana a Najeriya.

Majalisar Dattawa ta yi ƙari kan kasafin kuɗaɗen ne bayan da wasu ma’aikatu da hukumomi su ka gabatar wa majalisa ƙarin buƙatun kuɗaɗe, waɗanda ba a saka su a cikin Kasafin 2022 ba.

Ma’aikatun da su ka nemi kuɗaɗen sun haɗa da Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, wadda ta nemi naira biliyan 304 domin shirya zaɓen 2023. Sai kuma Hukumar Tsaro ta Sojoji, Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa, Ma’aikatar Harkokin Noma da Raya Karkara, Hukumar Leƙen Asiri, Ayyukan Majalisar Dattawa da Tarayya a Mazaɓu.

Sai kuma Ma’aikatar Ilmi, Ma’aikatar Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwa da kuma Ma’aikatar Harkokin Ruwa.

Tsakuren Jawabin Buhari Yayin Da Wa Kasafin 2022 Hannu:

Shugaba Buhari ya ce zai miƙa kasafin a hannun majalisa da wuri a farkon shekara.

Ya umarci Shugabannin Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya, Shugabannin Cibiyoyin Gwamnanti da na Ma’aikatun Gwamnati su haɗa kai da Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe, Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare, musamman su haɗa kai da Ofishin Kasafin Kuɗaɗe na Tarayya domin a cimma ayyukan da ake son aiwatarwa a cikin kasafin.

Asarƙalar Canje-canjen Da ‘Yan Majalisa Su Ka Yi Wa Kasafin 2022 -Buhari

Duk da yabon da Shugaba Buhari ya yi wa ‘yan majalisa, a ɗaya gefen kuma ya gigara masu zarto a agara, inda ya ce canje-canjen da su ka cusa cikin kasafin, abin damuwa ne ainun.

Kaɗan daga cikin canje-canjen sun haɗa da ƙara adadin kuɗaɗen shiga da ake sa ran tarawa da naira biliyan 400, adadin da Buhari ya ce ba su bayar da dalilin yin hakan ba.

Buhari ya yi ƙoƙarin cewa majalisa ta rage kuɗaɗen alawus ‘yan sanda, inda ta rage masu naira biliyan 15. Sannan an rage wa Sojojin Ruwa Naira biliyan 5 su ma.

“Wannan kuwa abin damuwa ne, saboda domin kuɗaɗen alawus ɗin jami’an tsaro batu ne da hukumomin su ke da haƙƙi a kai, kamar dai albashin su kenan.

“Sannan sun ƙara kuɗaɗen hidimar ofisoshi na wasu hukumomin gwamnati da Naira biliyan 21.72, yayin da su ka zabtare Naira biliyan 1.96 daga wasu ma’aikatun gwamnati ba tare da wata hujja ba.

“Sun ƙara Naira biliyan 575.63 a kan kuɗaɗen manyan ayyuka, inda su ka koma Naira tiriliyan 5.47 daga naira tiriliyan 4.89.”

Majalisa ta rage Naira biliyan 12.6 na kuɗaɗen Ma’aikatar Sufuri; ta rage Naira biliyan 25.8 a ɓangaren Shirin Gyaran Ayyukan Lantarki wanda ke ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe; Majalisa kuma ta rage Naira biliyan 14.5 daga ayyukan Ma’aikatar Gona da Bunƙasa Karkara. Sannan kuma majalisa ta ƙirƙiro sabbin ayyuka 1,500 a ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Gona da sauran hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar.

Buhari ya kuma nuna damuwa da wasu Naira biliyan 36 da Majalisa ta ƙara a cikin kasafin ayyukan mazaɓu na ‘yan majalisa.