GWAMNONIN KANO, KATSINA DA KADUNA A 2021: ‘Da burgu da zomo da kurege, kowane na shi hali ya ke bamban’

Gwamna El-Rufai: Kowa Ya Ci Zomo Ya Ci Gudu:

A cikin shekarar 2021 dai a Arewa, kafin ka samu gwamna mai baƙin jinin Nasir El-Rufai, sai ka yi zurfin bincike. To amma mutum ba zai gane Malam ya na da farin jini fiye da tunanin mai tunani ba, sai ya shiga garin Kaduna har ya ga yadda ya gyara garin.

Adalcin da za a yi wa El-Rufai, shi ne a kewaya a cikin mutane a ji ra’ayoyin su. Hakan zai sa mai karatu ya fahimci cewa a duk inda mutum ɗaya ya soki Malam, to mutum ɗaya zai jinjina masa. A inda gungun mutum 10 suka ragargaje shi, to wani gungun mutum 10 za su gode masa.

Shekaru biyu da suka gabata El-Rufai ya sha yin ƙorafi kan matsalar ƙarancin kuɗaɗen shigar jihar, inda ya ce mafi yawan kuɗin da Jihar Kaduna ke karɓa daga Gwamnatin Tarayya, duk wajen biyan albashin ma’aikata su ke tafiya.

“To ya kamata a sani cewa ba biyan albashi ne kaɗai aikin gwamna ba.” Inji Malam.

Ga wanda ya shiga Kaduna, ya karaɗe kudu da arewacin garin da kuma tsakiyar sa, zai tabbatar da cewa Malam Nasir ba aikin biyan albashi kaɗai ya yi ba. Nasir ya yi gyara, ya yi ayyuka, kuma ya yi gyare-gyaren da duk da dai a bisa ƙa’idar doka ya yi su, hakan bai hana mutane da dama su riƙa sukar sa ba.

Babban abin da ya janyo wa El-Rufai suka shi ne rushe gidaje musamman na marasa ƙarfi. Yayin da ɗimbin masu gidajen da aka rushe su ka karɓi diyya, Nasiru ya riƙa rusa gidajen da aka gina ba bisa ƙa’ida ba. Wannan kuma aiki ne da ya yi a matsayin ‘tsumagiyar kan hanya, ki fyaɗi babba, ki fyaɗe yaro.’

Samun gwamna kamar El-Rufai mai jimirin jure dafin kibiyar masu ragargazar sa akwai wahala. Sukar da ake yi masa ba ta sa ya fasa aiwatar da ayyukan raya al’umma wanda ya ke ganin idan ya aiwatar, to waɗanda za su amfana za su fi waɗanda ke sukar sa yawa matuƙa.

A wannan saura shekara ɗaya da rabi da su ka rage wa Gwamna El-Rufai a kan mulki, zai yi kyau Malam ya bijiro da wasu ayyukan da talakawa ne kaɗai za su fi cin moriyar su. Irin waɗannan ayyuka sun haɗa da giggina wuraren ƙananan sana’o’in matasa, samar da wuraren sayar da kaya ga waɗanda aka kora daga gefen titi.

Irin waɗannan masu ƙananan sana’o’i ne aka riƙa bi ana yi masu kamfen a 2015. Kuma su ne dai su ka yi zaɓen da aka yi nasara. Domin wasu manyan wuraren kasuwancin da masu hali ke cin moriya a yanzu, yawancin masu harkoki a wuraren da masu zuwa a matsayin kwastomomi, duk su na gida zaune talakawan da aka kora gefen titi suka zaɓi gwamnati.

Gwamna Masari: Kurege Mai Rami Ɗaya Ƙofa Bakwai:

Tun lokacin da Gwamna Aminu Masari ke kamfen a ƙarshen 2014 da farkon 2015 aka fahimci wani abu daga gare shi. An lura ɗan siyasa ne mai dabara irin ta kurege.

Kurege ne zai gina rami, amma sai ya yi mashigar ramin ko mafitar sa kamar ƙofa bakwai a kusarwa daban-daban.

Marigayi Musa Ɗanƙwairo Maradun ya fassara mana irin su Masari a cikin waƙar, “Gagarau Mai Jiran Daga, Ali Na Magaji Ci-fansa”:

“Da burgu da zomo da kurege,
Kowane na shi hali shikai bamban,
Burgu shi ka rami cikin ƙunƙu,
Zomo shi ka kurhi gaton kalgo,
Na ga kurege ya yi ɓannag gaba,
Sai yai jawabi nai shi kau,
Na rega ka maigida,
Kai wawa in nish shiga ban hitowa nan,
Ta inda dun nish shiga ban hitowa nan,
Sai ya yi ɓula tai can daban,
In nan rwakatan in hicewa can.”

A farkon kamfen ɗin Masari a zaɓen 2015, ya yi amfani da mawaƙi Rarara ɗan yankin su a Katsina, ya riƙa nuna matsalar rashin tsaro da gazawar PDP a Katsina. Masari ya samu damar da sai da ta kai ya maida ‘yan PDP tamkar mujiya a lokacin kamfen da lokacin zaɓe.

A lokacin kamfen, Masari ya yi alƙawarin idan ya hau mulki zai sayar da sabon Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, wanda gwamnatin PDP ta gina. Ya ce asarar kuɗi ne kawai gina gidan.

Sai dai kuma abin mamaki, Masari bai sayar da gidan ba. Har kuɗi ya ƙara kashe wa gidan kafin ya shiga ciki ya tare, bayan ya zama gwamna.

Mu gangaro kan matsalar tsaro a Katsina. Masari ya fara ƙoƙarin da sai da ta kai shi ya na taron ganawa da gogarma-gogarman ‘yan bindiga domin su ajiye makamai. Har yanzu duniyar soshiyal midiya cike ta ke da hotunan Masari tare da tantirin ɗan bindiga Buharin Daji.

Sai dai kuma tabbataccen lamari ne cewa ɓarnar ‘yan bindiga a jihar Katsina ta fi muni a zamanin mulkin Masari, fiye da zamanin PDP.

Duk wata hikima da dabara da tsare-tsare sun ƙare bayan Masari ya kori PDP a Katsina saboda rashin tsaro. A yau ƙarshen 2021, bayan shekaru kusan bakwai kan mulki, Masari ya nuna wa al’ummar jihar Katsina cewa gwamnatin su ba za ta iya kare talakawa daga hare-hare da kashe-kashen ‘yan bindiga ba.

Yayin da ya ce kowa ya nemi bindiga ya kare kan sa, su kuma talakawa na mamakin yadda shi gwamna zai fadi haka, domin jami’an tsaron da ya ce sun yi ƙaranci, su ne dai ke kare shi a duk inda ya ke. Ga abin da Gwamna Masari ya ce, wanda hakan tantagaryar gazawar gwamnatin tarayya da ta jiha ce, wajen kare rayuka da dukiyar Katsinawa masu Shugaba Buhari sukutum.

“Kowa Ya Tanadi Bindiga Ya Kare Kan Sa, Wanda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Ya Mutu Shahidi” -Masari:

Kusan shekaru bakwai bayan hawa mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, ɗan Jihar Katsina, rashin tsaro na ƙara dagulewa a jihar sa ta haihuwa, har ta kai ga Gwamna Aminu Masari ya umarci ɗaukacin ‘yan jihar cewa kowa ya sayi bindigogin kare kan sa daga ‘yan bindiga.

Da ya ke jawabi, Masari ya ƙara jaddada cewa jami’an tsaro su kaɗai ba za su iya magance wannan gagarimar matsala ba.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Gidan Gwamnatin Katsina mai suna Muhammadu Buhari House, Masari ya ce jami’an tsaro sun yi ƙaranci matuƙa, ta yadda yawan su ba zai iya daƙile ‘yan bindiga ba.

“Musulunci ma ya yarda mutum ya kare kan sa. Tilas mutum ya tashi ya kare kan sa, ya kare iyalin sa da dukiyar da. Idan ka mutu wajen kare kan sa ko iyalin ka ko wata dukiyar ka, to an kyautata maka cewa ka mutu shahidi.

“Abin mamaki ne a ce ɗan bindiga ya mallaki bindiga, shi kuma mutumin ƙwarai mai ƙoƙarin kare kan sa da iyalin sa a ce ba shi da bindiga.” Haka Masari ya bayyana.

Masari ya ce gwamnatin jiha za ta taimaki waɗanda ke so su mallaki bindiga da nufin kawo ƙarshen wannan matsalar tsaro.

“Za mu goyi bayan masu halin da su ka bijiro domin su taimaka wa al’umma su mallaki bindigogi.

“Lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya zama shugaba, ya yi ƙoƙarin ƙara yawan jami’an tsaro. Amma duk da haka ba su wadata ba.

“Ku lissafa, ‘yan sanda nawa mu ke da su a ƙasar nan? Sojojin ƙasar nan dududu guda nawa ne?

“Kai ko ma cewa aka yi kowane ɗan sanda ya koma jihar sa, hakan ba zai magance matsalar ba. Saboda haka idan mu ka riƙe hannu mu ka ce mu zura ido, to kan mu kawai za mu ƙwara.” Inji Masari.

Masari ya bada shawara cewa aikin ‘yan sanda ne su yi rajistar bindigogin da fararen hula za su saya, domin su tabbatar da cewa an yi aikin da ya dace da su.

Gwamna Ganduje: Gandun aiki, Ganduje marmari daga nesa:

Daga lokacin da Gwamna Abdullahi Ganduje ya hau mulki cikin 2015 har zuwa 2021 ya kasance mai amfani da ƙarfin mulkin sa da ƙarfin ‘yan siyasar da ke kewaye da shi ya na yadda ya so. Sai abin da ya dama za a sha a Kano, da daɗi ko ba daɗi, kuma a haƙura.

Ganduje ya yi mummunar ɓatawa da ubangidan sa, tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso. Ya kekketa Kano ya ƙirƙiro ƙarin masarautu, ya tsige Sarki Muhammadu Sanusi II. Ganduje ya gama da ‘yan adawa a zaɓen Gama.

A gefe ɗaya kuma shugaban APC Abdullahi Abbas ya riƙa fige duk wata kazar adawa da ran ta. An wayi gari kalaman da ke fitowa daga bakin wasu manyan ‘yan siyasar Ganduje ko a filin kiɗan tauri bai kamata a riƙa jin su ba. Saboda kalamai ne na ‘mutakabbiranci’.

Ganduje ya sha fama kuma ya sha tsangwama a kan faifan bidiyon dala. Amma duk waɗannan ba su karya masa lago ba. Har sai kusan ƙarshen shekarar 2021, inda kotu ta riƙa kwarara masa bokitan ruwa, har ta kai shi ga yin laƙwas. Ƙarshen tika-tika dai, a ƙoƙarin Ganduje na yin ƙarfa-ƙarfa lokacin zaɓen shugabannin jam’iyya, ta kai shi ga asarar ragamar jam’iyyar baki ɗaya.

Guduma 7 Da Kotu Ta Buga Bisa Kan Ganduje Cikin Watan Nuwamba:

A bisa dukkan alamu Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya fara hango ƙarshen zangon mulkin sa na biyu, tun yanzu sama da shekara ɗaya kafin ya fita daga gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Ganduje wanda har yau fatalwar zaɓen ‘inkwankulusib’, wanda aka ce bai kammalu ba ba ta fice daga cikin ƙwanƙwaman kan sa ba, a ɗaya gefen kuma har yau akwai kurwar zargin cushe-cushen miliyoyin daloli a kan sa.

Waɗannan fatalwa da kurwa za su daɗe a jikin sa kafin ya samu makarun da zai karya su a fitar masa da su, bayan ya sauka daga mulki, cikin 2023.

Guduma 7 Kan Ganduje:

Cikin watan Nuwamba, Gwamna Abdullahi Ganduje ya biya tarar sa da kotu ta ci har naira 800,000 saboda ya ɓata wa Ja’afar Ja’afar suna.

Ja’afar shi ne ya fallasa zargin Ganduje da aka nuno shi ya na cusa daloli aljihu.

Wannan kuɗi dai tuni har Ja’afar ya ɗora naira 200,000 a kai, sun cika miliyan ɗaya, kuma ya ce a yi ayyukan taimakawa ga mabuƙata da kuɗin.

Guduma ta biyu a kan Ganduje ita ce soke zaɓen APC ɓangaren Abdullahi Abbas da Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yi a ranar 30 Ga Nuwamba.

Mai Shari’a Hamza Mu’azu ya ce shugabannin APC ta ɓangaren tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau ne halastattun shugabanni, a ƙarƙashin Haruna Ɗanzago.

Guduma ta uku da kotu ta ranƙwala wa Ganduje, ita ce umarnin da kotun ta bayar cewa kada ɓangaren Ganduje ya sake yin wani zaɓen shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Kano.

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta ɗirka wa Ganduje kulki na huɗu, inda ta haramta korar da Gwamnatin Jihar Kano ta yi wa Murabus Sarki Muhammadu Sanusi II.

Kotun ba ta tsaya nan ba sai da ta muƙa wa Ganduje kulki na biyar, inda ta ce ya biya Sanusi diyyar tauye masa ‘yanci har naira miliyan 10.

Guduma ta shida ita ce umarnin da kotun ta bayar cewa Sanusi na da ‘yancin dawowa Kano ya ci gaba da zaman sa. Ko kuma ya riƙa shigowa birnin a duk lokacin da ya ga dama.

Kotu ta ɗirka wa Ganduje guduma ta bakwai, inda ta umarce shi da ya buga roƙon neman afuwa ga Murabus Sarki Muhammadu Sanusi II a jaridu biyu na ƙasar nan.

Waɗannan batutuwa duk a cikin watan Nuwamba su ka faru, waɗanda ko shakka babu dukkan su babu wanda Ganduje zai yi farin ciki da shi. Domin tuni har ya fara gaganiyar tattara bayanan ɗaukaka ƙara.

Idan za a iya tunawa, Babbar Kotun Abuja ta ƙara jaddada shugabancin Haruna Ɗanzago a APC ta Jihar Kano. Tuni Ganduje ya saduda, ya ce wa magoya bayan sa su bi umarnin kotu.

Shekarar 2021 dai ta bar tarihi. Kuma tabbas za a ƙara kafa wani tarihin a Kano da Kaduna da Katsina a cikin 2022.