Kashi 1 bisa 6 na ilahirin balagaggun duniya na fama da ciwon kasa haihuwa – UN

Daraktan Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WHO), Tedros Ghebreyesus, ya bayyana cewa kashi 1 bisa 6 na ilahirin balagaggun mutanen duniya su na fama da rashin iya ɗaukar ciki idan mata ne. Idan maza ne kuma su na da matsalar kasa ɗirka wa mata ciki.

Ghebreyesus ya yi wannan bayanin a wurin taron Bibiyar Illolin cutar Coronavirus, a Geneva.

Wannan bayanin na Shugaban WHO, ya tabbatar cewa kashi 17.5 na ilahirin balagaggun cikin duniya, su na fama da matsalar kasa haihuwa.

Wannan adadi ya na nufin kashi 6/100 na balagaggun mutanen duniya ba su iya haihuwa kenan.

Daga nan sai ya yi kira da a samu sauƙin kai wa jiha ga magungunan da za a su bijiro da kayan magungunan da za su iya samar masu damar iya yin ciko ko kuma ɗaukar ciki.

Hakan ya ce wannan ciwo ya na cikin manyan attajirai, masu halin halin yau da kullum da kuma waɗanda ke neman abincin cin yau da na gobe.

WHO ta fassara “kasa ɗaukar ciki” da cewa yanayi ne wanda idan miji da mata su ka shafe watanni 12 cur su na jima’a a kai a kai, kuma matar ba ta yi ciki ba.