Yadda Ƴan bindiga suka kashe ‘yan sanda uku a jihar Kogi

Wasu ‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda uku a ƙaramar hukumar Adavi dake jihar Kogi a cikin ƙarshen makon jiya.
Komishinan ‘yan sandan jihar Edward Ebuka ya sanar da haka a wata takarda da kakakin rundunar William Ovye-Aya ya raba wa manema labarai a garin Lokoja.
Ebuka ya ce jami’an tsaron ‘yan sandan sun rasa rayukan su a lokacin da suka artabu da mahara bayan sun yi musu diran bazata a caji ofis ɗin su a Adavi.
” Ko da maharan suka danno caji ofis ɗin ba su sha dadaɗi ba domin kuwa da yawa daga cikin su sun arce ne da muggan raunuka a jikkunan su na wuta da suka sha.
Kwamishinan ya aika da ta’aziyar sa ga iyalan ‘yan sanda uku da suka mutu a dalilin wannan arangama.
Ya kuma yi kira ga mutanen Adavi da su Yi gaggawan kai karan duk wanda suka gani da raunin harsashi a jikinsa ga rundunar ƴan sanda mafi kusa.