AMAI DA GUDAWA: Mutum 595 sun rasu a Jigawa a shekarar 2021

Ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa ta bayyana cewa mutum 21,877 sun kamu sannan mutum 595 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar amai da gudawa a shekarar 2021.

Babban sakataren ma’aikatar Salisu Mua’zu ya sanar da haka a taron da ya yi da manema labarai a jihar a makon jiya.

“Cutar amai da gudawa na da alaka da rashin tsaftace jiki da muhalli sai dai abin takaici ne yadda mutane ke kamuwa da cutar bayan kokarin da gwamnati ta yi wajen samar da tsaftataccen ruwa a jihar.

Ya ce ma’aikatar sa ta dauki matakai da za su taimaka wajen ganin an dakile yaduwar cutar a jihar a wanna shekara, 2022.

“Damina na sauka akwai ma’aikatan mu da za mu da za su taimaka wajen wayar da kan mutane sanin hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.

Mu’azu ya ce a shekarar 2021 gwamnati ta yi wa mutum 946,325 da mutum 904, 169 allurar rigakafin cutar a kananan hukumomin Birnin Kudu, Dutse da Hadejia.

“A shekaran 2021 gwamnati ta yi wa yara 1,720,742 da yara 1,782,026 ‘yan ƙasa da shekaru biyar allurar rigakafi a Yuni da Yuli.

Idan ba a manta ba a watan Nuwanba 2021 hukumar NCDC ta bayyana cewa cutar amai da gudawa ta yi ajalin mutum 3,566 daga cikin mutum 103,589 din da ake zargin sun kamu da cutar a jihohi 32 da Abuja.

NCDC ta ce jihohin Bauchi dake da mutum 19,470 da suka kamu da cutar Jigawa -13,293, Kano -12,116 da and Zamfara – 11.918 na daga cikin jihohin da suka fi fama da cutar a kasar nan.

Rage yawan mutuwar mata da yara kanana

Domin rage yawan mutuwan mata da yara kanana a jihar gwamnati ta tsara Shirin da zai taimaka wajen daukan mata masu ciki daga kauyukan dake da wahalar shiga zuwa asibiti.

Mu’azu ya ce gwamnati ta kashe sama da Naira miliyan 8.7 domin shirin ya fara aiki sannan ta dauki direbobi 600 saboda shirin.

“A dalilin Shirin kula da mata masu ciki da yara kanana kyauta dake aiki a asibitoci 23 a jihar mutum 1,348122 na samun kula kuma gwamnati ta kashe Naira 751,212,291 a shirin.