Yadda Ƴan bindiga suka kashe mutum uku suka yi garkuwa da mutane da dama a jihar Katsina

A safiyar Laraba ne ƴan bindiga suka kashe mutum uku inda a ciki akwai wani kansila mai suna Nasir Magaji a kauyukan dake karamar hukumar Malumfashi jihar Katsina ranar Laraba.
Mazauna karamar hukumar sun tabbatar cewa ‘yan bindigan sun yi garkuwa da mutane da dama inda a ciki akwai mata biyu.
Dutsen Reme Low-Cost Funtua, Gozaki dake Kafur da Dan Rimi na daga cikin wuraren da ‘yan bindiga suka kai farmaki.
Wani mazaunin Dutsen Reme Abdurrahman Aliyu, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun shigo cikin tsakar dare suka yi kan mai uwa dawabi da harbe-harbe.
“Wannan shine karo na biyu da ‘yan bindigan ke kawo wa kauyen mu hari a cikin wata daya. A wannan dare ina zauna ina kallon talabijin ina jiran karfe uku na dare ya yi na yi salloli sai na ji karar ruƙugin bindiga. Daga nan sai wani dan uwana wanda shi dan sanda ne ya kira ni a waya ya fada mun cewa ‘yan bindiga sun shigo kauyen.
“Daga baya sai ya kara kira na ya ce mini jami’an tsaro da suka hada da ƴan sanda da sojoji sun fatattake su amma an kashe wani mai suna Malam Buhari.
“Maharan sun kashe Malam Buhari a kofar gidan sa.
Kauyen Gozaki
Mazauna ƙauyen Gozaki sun bayyana cewa ƴan bindigan sun yi garkuwa da matan kansila su biyu, daga baya sai suka dawo da matan, suka harbe kansilan.
Maharan sun kashe kansilan ba tare da sun saci komai daga gidan sa ba.
Kansilan ya wanda kwanakin sa biyu kenan da zama kansila ya rasu a asibitin Kafur.
Kauyen Dan Rimi
Wani dan jarida dake zama a kauyen Aliyu Musa ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da mutane da dama har da mata biyu.
“Zuwa yanzu na ga mutum sama da hamsin da suka gudo zuwa Malumfashi sannan wasu magidanta biyu sun ce maharan sun tafi da matan su biyu.
“Sai da yamma hankalin kowa ya kwanta za mu iya sanin adadin yawan mutanen da aka yi garkuwa da su domin wasu sun gudu zuwa daji.
Zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan jihar bata ce komai ba game da harin sannan kakakin rundunar Gambo Isa bai amsa wayarsa ba.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suka yi kaurin suna da hare-haren ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.
‘Yan bindigan na garkuwa da mutane domin karban kudin fansa, saka wa kauyukan haraji, sace wa mutane dabobbin su da sauran kaya masu daraja, kisa da dai sauran su.
Maharan na cin karen su ba babbaka a yankin sannan gwamnati duk da yi wa mutane alkawarin kare rayuka da dukiyoyin su sun ƙasa yin komai a kai.