BINCIKEN ƘWAƘWAF: Yadda sakaci ya haddasa cutar tarin TB ta kashe ɗaurarru birjik a kurkukun Katsina

Aƙalla dai mutum 20 ne suka mutu sanadiyyar cutar tarin TB, yayin da wasu ɗaruruwa suka kamu a gidan kurkukun Katsina. Waɗanda ke da cikakkar masaniyar ɓullar mummunar cutar ce suka tabbatar wa PREMIUM TIMES haka.

Sun bayyana cewa matsalar ta faru sanadiyyar wawure kuɗaɗen kula da ɗaurarru da ake yi, sai kuma sakacin yadda aka wofintar da tsarin kula da lafiyar ɗaurarru a kurkukun, wanda ya kai shekaru 104 da ginawa.

Manyan jami’ai, ciki har da waɗanda haƙƙin kula da gidan kurkukun ke wuyan su, duk sun yi ƙoƙarin binne wannan ɓarnar kisa da cutar TB ta yi a kurkukun, don kada a fallasa su.

Wannan jarida ta kuma ta gano cewa an lulluɓe jami’an da ya kamata su nan da matsalar, waɗanda su ke da alhakin kai rahoto a gaba. Maimakon a sanar da su da wuri, sai aka bar su a duhu.

Wani babban jami’in da aka ɓoye wa afkuwar annobar tarin na TB, ya yi mamakin cewa “ta yaya wannan abu zai faru ba a sanar da ni ba? Ai kuwa ba zan yi shiru ba.”

An gina kurkukun Katsina cikin 1918 domin a riƙa tsare ‘yan bursuna 300 a cikin sa. Amma a yanzu haka akwai ‘yan bursuna ɗaurarru da masu jiran a yanke masu hukunci a cikin kurkukun za su kai mutum 900. Haka wani jami’i ya shaida.

Wani ƙwararren jami’in lafiya ya ce rayuwa irin wurin da ke da cukoso kamar kurkukun Katsina zai iya sa mutum ya kamu da cutar tarin TB.

Walle-wallen da ake yi da shari’u a kotu ya haifar da yawan cinkoson waɗanda ke jiran a yanke masu hukunci. Hakan ne kuma ke haifar da kamuwa da cututtuka a gidajen kurkuku, musamman cutar TB.

“Jami’an gidajen kurkuku na haɗa baki da DPO na ‘yan sanda a kamo mai tsautsayi, a turmusa shi gidan kurkuku. Wasu jami’an kurkuku na tara mutane da yawa don su riƙa karɓar kuɗaɗen kula da ɗaurarru masu yawa.” Haka majiyar da ta ce a sakaya sunan ta.

Ɓullar Cutar Tarin TB A Kurkukun Katsina:

A farkon watan Afrilu ne mutum 71 da ke tsare a kurkukun Katsina suka kamu da cutar tarin TB a wannan kurkukun, kamar yadda wani wanda ya san dukkan abin da ke faruwa a ciki ya sanar da wakilin mu. Kuma ya ƙara da cewa zuwa tsakiyar wata waɗanda suka kamu da cutar sun kai mutum 89.

Ana hasashen ma cewa waɗanda suka kamu ɗin sun zarce wannan adadi, idan aka yi la’akari da irin taɓarɓarewar kiwon lafiya da rashin kulawar da ake masu.

“Tarin TB cuta ce da ake warkewa idan ana kula da shan magani. Amma ganin yadda kula da lafiya, rashin magunguna da kuma ƙarancin abinci suka yi katutu, hakan zai iya haddasa yaɗuwar cutar da kuma kisa.” Haka wata majiya ta shaida wa wakilin mu. “Ai mummunan al’amari haka yake ta faruwa a cikin kurkukun.”

Kakakin Hukumar Gidajen Kurkuku na Ƙasa, Francis Enobore, ya ce ɓarkewar cutar TB ɗin tun a cikin watan Janairu ne ta faru, kuma mutum 7 suka mutu.

“Daga aka daƙile cutar ta hanyar samar masu magunguna. Ba a ƙara samun ɓullar cutar ba, sai cikin Afrilu.”

Sai dai kuma binciken da muka bankaɗo ya nuna cewa Enobore ya binne gaskiyar abin da ya faru. PREMIUM TIMES ta ga kwafen takardun da ke tabbatar da yawan ɗaurarrun da suka kamu a cikin watan Afrilu, kuma aka kwantar da su asibiti. Yanzu haka ma ba a sallame su ba.

Sannan kuma PREMIUM TIMES ta mallaki hotunan waɗanda suka mutu bayan kamuwa da tarin TB da kuma waɗanda ke kwance raɓe-raɓe a asibiti saboda kamuwa da cutar.

Da yawan masu fama da cutar kwance suke a kan tabarmi, ba kan gadajen asibiti ba, kuma ko ƙarin ruwan leda ba a samu sukunin maƙala masu ba.

Kaɗan daga cikin su ne ke kan gadon asibiti. Waɗanda ke kan gadon ne suka samu gatan ɗaura masu ruwan leda. Amma duka waɗánda ke ƙasa kan tabarma, ko ruwan ledar ba su samu an ƙara masu a jikin sa ba.

Bincike ya nuna ɗaurarru a gidajen kurkukun Arewacin Najeriya ana ciyar da su ne ɗan abincin da ake cewa ‘ci-kar-ka-mu’.

Ko na ƙasar ma baki ɗaya abin da ake kashe masu a hukumance bai wuce Naira 750 kowane mutum ɗaya ba a kullum.

A cikin Naira 750 ɗin ma, majiyar da ta nemi a sakaya sunan ta, ta tabbatar da cewa wasu jami’an kurkukun na zabge kusan kashi 30 bisa 100 na naira 750 ɗin, su bai wa ‘yan kwangilar abinci sauran kuɗin su ciyar da ɗaurarrun.

Kafin 2021 dai Naira 450 ne ake kashe wa kowane ɗaurarre a kurkuku. Sai cikin 2021 ne aka maida kuɗin naira 750.

Ba kamar ɗaurarrun da ke Arewa ba, su waɗanda ke tsare a yawancin garuruwan kudancin Najeriya na samun gata daga waje. A kan samu ƙungiyoyi, coci-coci da masallatai na kai tallafi, agaji ko gudummawar abinci har cikin kurkuku.