Yadda Ƴan bindiga suka kashe mutum 7 suka babbake gidaje 250 a jihar Filato

Ƴan bindiga sun kashe mutum 7 kuma sun babbake gidaje 250 a masarautar Miango dake karamar hukumar Bassa jihar Filato.
Ƴan bindigan sun kai wa masarautar hari ne a daren Asabar.
Sakataren yaɗa labaran kungiyar Iregwe Davidson Malison ya sanar da haka ranar Lahadi a garin Jos.
Malison ya ce maharan sun lalata gonaki sama da 40 a masarautar.
“Baya ga raunin da suka ji wa mutane da dama a, maharan sun saci kaya da dukiyoyin mutane a wannan hari.
“Maharan sun dauki tsawon awa daya suna kona gidajen mutane a kauyukan Zanwra, Nche-Tahu, Rikwe-Rishe A da B da Ri-Dogo, Nchu-Nzhwa ba tare da jami’an tsaro sun kawo wa mutane ɗauki ba.
Malison ya yi kira ga gwamnati da ta aiko da ƙarin zaratan jami’an tsaro domin kare rayukan da dukiyoyin mutane a masarautar su.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ubah Ogabawanda ya tabbatar da aukuwar wannan hari, ya kuma ce an aika ƙarin jami’an tsaro domin samar da tsaro a masarautar Miango.
Jihar Filato na daya daga cikin jihohin Arewa dake fama da hare-haren ƴan bindiga da mahara a kasar nan.
Sauran jihohin Arewa da wannan ibtilai na rashin tsaro ya yi tsanani ya haɗa da jihohin Kaduna, Zamfara da Katsina.