Kotu ta warware kullin auren da ya shekara 48 saboda rashin jituwa wajen saduwa

Kotu dake Igando a jihar Legas ta warware auren shekara 48 dake tsakanin Mojidi da Tolu saboda Tolu ta na hana mijin nata yin jima’i da ita har na tsawon shekara 10.
Alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya raba auren ne bayan Mojidi ya yi watsi da kokarin daidaita su da kotu da mutane suka yi kokarin yi.
Alkalin kotun Koledoye ya yanke hukuncincin Mojidi ya biya Tolu Naira 250,000 na rabuwan aure sannan ya kara bata wasu kudin naira 250,000 kudin da za ta biya kudin haya da shi.
Mojidi mai shekaru 72 wanda makaniken mota ne ya shigar da kara a kotun yana karar matarsa cewa ta hana shi kusantar sa na tsawon shekaru 10.
“Na takura matuka sannan a duk lokacin da na kawo ‘yan mata na gida domin mu dan wataya ko mu shakata sai Tolu ta kore su, sannan kuma ita ba zata yardar min in shakata da ita ba.
Ya ce matarsa ta yi kokarin kashe shi ta hanyar zuba masa guba a abinci da yin tsafe-tsafe.
“Tolu ta yi mini tsafi har sau biyu domin ta kashe ni, ta kuma zuba mun guba a abinci sannan ta yi kokarin hana ni haihuwa amma duk Allah ya sa na yi nasara akan ta.
“Tolu har magani ta zuba a shago na domin ta kora min kwastamomi masu kawo gyaran mota.
“Matata ta daina wanke mun kaya shekaru 27 kenan sannan kuma ta na haka don gaje duk kadarorina idan na mutu.
“A gaskiya Ina dana sanin auren Tolu da na yi domin da ban aure ta ba da na ci gaba a rayuwa fiye da haka.
Ita kuwa Tolu Mai shekaru 65 ta roki kotu da kada ta raba auren ta saboda tana son mijinta.
Ta ce ta auri Mojidi a shekarar 1973 kuma sun haifi ‘ya’ya 10 tare.
Tolu ta ce tun a lokacin da suka yi aure bata kashe shi ba sai yanzu da suka tsufa tare suka haifi ‘ya’ya 10 tare ne za ta kashe shi.
Ta ce Mojidi makaryaci ne sannan yana neman ya sake ta ne saboda ta yi masa tsufa.