YA GUDU BAI TSIRA: Shari’ar Saminu Turaki ta koma sabuwa, bayan tsaikon shekara 14

Ƙarshen tika-tika dai an ce tik! Bayan shekaru 14 ya na ƙin halartar zaman kotu, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Saminu Turaki ya bayyana a karon farko cikin shekaru da dama.

Turaki ya bayyana a Babbar Kotun Tarayya ta Dutse, babban birnin jihar Jigawa, a ranar 7 Ga Disamba, domin amsa tuhuma 37 na wawurar kuɗaɗe wadda ake yi masa tun shekaru 14 baya.

Zaman kotun na ranar 7 Ga Disamba dai an zauna ne a gaban Mai Shari’a Hassan Dikko.

An maida shari’ar a hannun Hassan Dikko, bayan mai shari’a na farko S. Yahuza ya yi ritaya daga alƙalanci.

Ritayar da Yahuza ya yi ce ta sa aka ce a sake shari’ar tun daga farko a hannun Dikko, bayan Yahuza ya fara shari’ar tun cikin 2007.

Sake gabatar da Saminu ke da wuya a ranar 7 Ga Disamba, sai ya shaida wa kotu cewa bai aikata laifuka 32 da ake tuhumar sa ba har guda 32.

Kotu ta bada belin Saminu a kan kuɗi naira miliyan 100, sannan aka sa ranar 24 Ga Fabrairu, 2022.

Yanzu dai shekaru 14 kenan da fara wannan shari’a, wadda aka faro tun bayan kammala wa’adin sa na gwamnan Jigawa.

Cikin 2007 ne aka gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Binta Nyako. EFCC ta kama shi kuma ta gabatar da shi tare da tuhumar sa da aikata laifukan wawurar kaɗaɗe har tuhuma 32, a ranar 13 Yuli, 2007, watanni biyu bayan saukar sa daga mulki.

An zargi Saminu Turaki tare da wasu mutane da satar naura biliyan 37.

An maida shari’ar Saminu Turaki a Babbar Kotun Tarayya da ke Dutse cikin 2011, bayan ya ƙalubalanci gufanar da shi da aka yi a Kotun Tarayya ta Abuja.

Saminu ya riƙa guduwa ya na tsilla-tsilla, har sai a ranar 4 Ga Yuli, 2017 da aka damƙe shi a wurin wani taro a Abuja.

A lokacin Mai Shari’a Yusuf Halilu ya bada belin Saminu kan naira miliyan 500, kuma aka nemi ya ajiye fasfo ɗin sa na fita waje a kotu a ƙarƙashin Mai Shari’a Nnamdi Dimgba, a ranar 28 Ga Yuli, 2017.

Belin sa na Naira miliyan 500 ne, amma masu beli mutum biyu, aka ce kowa ya ajiye naira miliyan 250,000.

Sannan kuma an umarci Saminu ya riƙa kai kan sa ofishin EFCC a ranar aiki ta farkon kowane sabon wata.

Bayan Saminu ya cika sharuɗɗan beli ne aka maida shari’ar sa zuwa Babbar Kotun Tarayya ta Dutse.