BANKWANA DA 2021: Alƙawurra 10 da gwamnatin Buhari da Jam’iyyar APC mai mulki suka kasa cikawa daga 2015 zuwa 2021

Daga ranar Asabar, 1 Ga Janairu 2022, zai kasance shekara ɗaya tal ta rage wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan mulki. Duk da saura shekara ɗaya da watanni biyar ya kammala wa’adin mulkin sa, a gaskiya watanni uku daga biyar ɗin duk a wurin kamfen ɗin sake zaɓe su ke tafiya. Ragowar watanni biyu kuma na tafiya ne wajen shirye-shiryen sauka daga mulki.

Buhari ya samu nasarar zama shugaba bayan ya ɗaukar wa ‘yan Najeriya alƙawurra da dama, na alwashin tsamo ƙasar nan daga cikin halin ƙuncin da masu adawa da PDP ke cewa Najeriya ta shiga a lokacin.

Tabbas kowa ya san a lokacin PDP an yi fama da matsaloli, musamman munanan hare-haren ƙunar-baƙin-wake a Arewacin ƙasar nan.

Alƙawurra 10 Da Har Yau Ke Rataye A Wuyan Buhari:

1. Korar Fatara Da Talauci: Gwamnatin Buhari ya ɓullo da shirye-shirye na raba wa talakawa kuɗaɗe, bayar da ramce ga manoma da samar wa matasa ayyukan N-Power. Sai dai kuma wasu tsauraran matakan da ya ɗauka, musamman kulle kan iyakoki da hana shigo da shinkafa, sun taimaka ƙwarai wajen ruruta tsadar kayan abinci a ƙasar nan.

Kusan duk wani nau’in kayan abinci da ake sayarwa kafin Buhari ya hau mulki cikin 2015, yanzu farashin sa ya nunka. Wani ma ya nunka sau uku ko sau huɗu.

2. Rashawa Da Cin Hanci: Irin yadda Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗaɗe na Tarayya ke ci gaba da bankaɗo yadda ma’aikatun gwamnati da hukumomi da wasu cibiyoyi ke karkatar da kuɗaɗe, ya nuna har yanzu a gwamnatin Buhari kamar ta PDP, cike ta ke masu badaƙala.

Shi kan sa yaƙi da cin hancin a zamanin gwamnatin nan ya sha karo da samun cikas, inda aka riƙa zargin Ministan Shari’a Abubakar Malami, aka sallami tsohon Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, kuma aka tsige Shugaban Kwamitin Yaƙi da Rashawa na Shugaban Kasa, wanda Buhari ya kafa a ƙarƙashin ofishin sa.

Da yawa dawo daga rakiyar yaƙi da ɓarayin gwamnati, ganin yadda da yawa waɗanda aka riƙa zagi a lokacin da Buhari ke kamfen, su ka koma APC har aka ba su muƙaman siyasa.

Har yau bayan shekaru bakwai, babu wani tsohon ministan PDP guda uku da ke tsare a kurkuku. Kuma babu gwamna uku gangariya da ke tsare a kurkuku. Kuma babu manyan ma’aikatan gwamnati 10 dindi waɗanda ke tsare a kurkuku.

3. Matsalar Tsaro: A gaskiya an samu ragin tashin bama-bamai bayan hawa mulkin Shugaba Buhari. To amma kuma har yanzu Boko Haram na ci gaba da kai munanan hare-hare a kan sojojin Najeriya. Har yau dai Boko Haram ke kai farmaki har sansanonin sojin mu.

Mafi yawan labaran da mu ke ji a Arewa maso Gabas, su ne Boko Haram sun kai wa Sojojin Najeriya hari, amma an fatattake su. Ba mu jin labaran sojoji sun kori Boko Haram, sun raka su har maɓuyar su, sun karkashe su a can.

Sannan kuma har yau Boko Haram na kai wa garuruwa da ƙauyuka hari.

3a. Bala’in ‘Yan Bindiga: Maimakon a ga Buhari ya tashi tsaye haiƙan ya magance matsalar ‘yan bindiga, sai ya kasance bala’in a kullum sai ƙaruwa ya ke yi a ƙarƙashin mulkin sa. Babu tsaro a jihar sa ta haihuwa, Katsina. Babu tsaro a Zamfara da Sokoto da Kebbi da Neja. Babu tsaro a wasu sassan jihar Kaduna da Arewacin Najeriya.

A karon farko tun bayan samun ‘yanci, taɓarbarewar tsaro ta haifar wa Bakatsine da Badauri da Zamfare da Basakkwace da Banufe yin hijira. Wasu ma a Jamhuriyar Nijar su ka yi dandazo.

Allah kaɗai ya san yawan mutanen da aka kashe a Katsina, mahaifar Buhari a tsaron shekaru shida da rabi da Buhari ke kan mulki. Kuma Allah kaɗai ya san waɗanda aka kashe a sauran yankunan Arewa.

4. Dawo da kamfanin jiragen sama ta ƙasa: Har yanzu dai jiya iyau. Sai dai mu ji a jawabai da hotuna amma har yanzu ba a kai ga tabbatar wannan magana shekaru bakwai kenan.

5. Rage Tsadar Fetur: Zuwa yanzu dai wannan alƙawari na Buhari bai ma kai tasirin mafarki ba. Baya ga ƙarin farashin fetur da aka samu a lokacin sa, a yanzu haka gwamnatin sa za ta cire tallafi a shekarar 2022, ta yadda litar fetur ɗaya za ta iya kaiwa N345.

6. Alƙawarin Gyaran Zaɓe: Wannan na daga sahun alƙawurran Buhari na farko. Sai dai kuma fatali da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe da Buhari ya yi kwanan baya, ya sa duk wani mai tunanin Buhari zai cika alƙawarin gyaran zaɓe ya daina wannan wannan mafarkin.

7. Alƙawarin Sauya Fasalin Najeriya: Wannan na daga cikin alƙawurran da shi da APC su ka yi kamfen cewa za su yi. Amma bayan an hau mulki cikin 2015 har zuwa yau, gwamnatin Buhari ta daina tayar da batun, kuma ba ta so ta ji ana tunatar da ita wannan alƙawari.

8. Alƙawarin Gyaran Matatun Mai: Wannan alƙawari tabbas APC ta yi kamfen da shi sosai, kuma ta karya lagon PDP ta hanyar yi wa talakawan Najeriya alƙawarin gyara matatun fetur na Warri, Fatakwal, Kaduna da Legas.

Shekaru kusan bakwai bayan mulkin Buhari ya ƙara narka biliyoyin kuɗaɗen gyara matatun mai, a yanzu dai alƙawarin ya zama tatsuniya.

Lamarin ya lalace har ta kai a yanzu gwamnatin Najeriya ta dogara ne da matatar mai wadda Dangote ke ginawa a Legas, domin ta riƙa samun fetur cikin sauƙi.

9. Alƙawarin Karya Darajar Dala: Buhari ya yi alƙawarin ƙara wa Naira daraja, yadda ko da ta ruƙume kokawa da dala, to ba za a ji kunya ba.

Maimakon haka, yayin da Buhari ya hau a lokacin da dala ɗaya ta na daidai da naira 197 zuwa 220. Amma a yanzu dala ɗaya ta kai naira 570.

10. Wasu Alƙawurra Da Dama: Irin waɗannan sun haɗa da alƙawarin sayar da bargar jiragen Fadar Shugaban Ƙasa, alƙawurran inganta lafiya, alƙawurran kewaye makarantun Arewa maso Yamma a gina masu katanta da waya da kuma sa masu ‘CCTV camera’ da alƙawarin kare ɗalibai daga sacewa, bayan an sace ɗaliban Chibok.

Maimakon a samu tsaro a makarantu, sai ya zama a tarihin ƙasar nan, a zamanin mulkin Buhari ne aka fi sace ‘yan makaranta ƙanana da manya zuwa har na jami’a.