Wutar Jahannama ce makomar duk ɗan Fanshon Kano da ya nuna rashin godiyarsa ga Kwankwaso

Tsohon ɗan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP a zaben 2019 Aminu Abdussalam ya zargi ƴan fanshon Kano da nuna rashin godiyar Allah.

Aminu ya ce ƴan fanshon da suka kai Rabiu Kwankwaso hukumar EFCC ba su kyauta sannan basu da godiyar Allah.

” A zamanin Kwankwaso ne yan Fansho suka samu walwala da karin kudi har naira 5000. Amma wa i sune kuma suke kai Kwankwaso kara ofishin EFCC.

” Kwankwaso yayi iya kokarin sa, duk wani ɗan fansho da bai gode masa ba, butulu ne wutar Jahannama ce makomarsa. Haka ne za a jejjefasu Jahannama saboda badu da godiyar Allah.

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin sammacin da hukumar EFCC ta yi sanata Kwankwaso a cikin wannan makon.

Duk da dai bai amsa kirar hukumar ba, bayanai da suka fito daga hukumar sun nuna cewa wasu ƴan fansho ne suka kai ƙarar sa hukumar suna bukatar hukumar ta taso keyar sa ya bayyana a gaban ta yayi bayanin yadda yayi da kuɗaɗen ƴan fanshon jihar.

Ana zargin sa da wawushe kuɗaɗen ƴan fanshon jihar a lokacin da yake mulki a jihar.

Wasu da dama na ganin cewa hakan maƙarƙashiya ce domin a kakaba wa Kwankwaso laifi dole domin matar abokin faɗar sa gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, Hafsat Ganduje da Ɗan ta sun cukuikuye cikin harkallar wasu kudade.

Hakan ya sa su ke ganin dalilin da ya sa EFCC ta gayyace Kwankwaso.