Al’ummar ƙauyen Sokoto sun kashe tare da kama ƴan bindiga da suka kai musu hari

Mazauna ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto, tare da haɗin gwiwar ‘yan banga sun kashe ƴan bindigar da suka kai hari a garuruwansu tare da cafke wasu.

Daily Star ta naƙalto wata majiya daga ƙauyen ta shaida mata cewa cikin ƙasa da awanni 24 da kai harin al’ummar garin suka bi diddigi tare da gano mafakan ƴan bindigan.

A wani faifan bidiyo dakw yawo, an ga maharan da aka kama kewaye da mutanen kauyen suna jiran jami’an tsaro su yi awun gaba da su.

Sai kuma a wasu hotunan da suma suke yawo an ga yanda fusatattun matasan garin suke ƙoƙarin banka musu wuta su ƙona su da rai.

An wallafa wannan Labari September 18, 2021 7:59 PM