WATANDAR NAIRA BILIYAN 656: Buhari ya raba wa kowace jiha naira biliyan 18.2

Majalisar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasa (National Economic Council), ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a bayar da naira biliyan 656 ga jihohin ƙasar nan 36, domin cike giɓin rashin nauyin aljihun asusun jihohi.

Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a ranar Alhamis, a wuri taron Majalisar Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasa ɗin, wato NEC. Matakimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo ne ya shugabanci taron, wanda aka yi ta intanet, kowa daga ofishin sa, shi ma daga ofishin sa ya jagoranci taron.

Minista Zainab ta ce an bai wa jihohi kuɗaɗen ne domin su biya basussukan da ake bin su daga ayyukan cikin kasafin kuɗin da ya shuɗe, na bara, wanda ya ce a yanzu haka ana bin jihohin bashin kuɗaɗen ayyukan da ba su biya ba.

Zainab ta ce za a bai wa kowace jiha naira biliyan 18.2.

Ta ce tuni Bankin Najeriya (CBN) na nan na ta ƙoƙarin fitar masu kuɗaɗen.

“Amma ba gaba ɗaya za a dumbuza masu kuɗaɗen ba. Za a raba wa kowace jiha na ta kason gida shida, kowane wata a ba ta kaso ɗaya, har tsawon watanni.

“An amince su biya kuɗaɗen cikin shekaru 30. Kuma sai bayan shekaru biyu nan gaba za su fara biyan kuɗin. Sannan kuma za a caji kowace jiha kuɗin ruwa kashi 9 bisa 100 na kuɗaɗen.