Labarin PREMIUM TIMES ya fargar da gwamnati, ta ware kashi ɗaya na kasafin kiwon lafiya don shirin kyayyade iyali

Bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ma’aikatar Kiwon lafiya ta ki samar da ko sisi a kasafin ta domin shirin bada tazarar haihuwa, gwamnati ta sanar da keɓe kashi ɗaya cikin kasafin kiwon lafiyar domin wannan shiri a ranar Alhamis.

A taron samar da musayan ra’sti da aka yi domin tsara hanyoyi da dabarun yadda za a inganta shirin kyayyade iyali da kuma bada tazarar haihuwa ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa gwamnati za ta ware kashi daya daga cikin kassafin kudin kiwon lafiya domin wannan shiri.

Ehanire yace gwamnati ta fitar da wannan sanarwa bayan mako daya bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ta ware wa wannan shiri kuɗi ba.

Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 816 wa fannin kiwon lafiya daga cikin Naira tiriyan 16.39 din da ta ware a kassafin kudin shekarar 2022.

Taron samar da dabarun bada tazarar haihuwa FP2030

An tara dala biliyan 3.1 a dalilin baye-bayen da kasashen duniya da kungiyoyin bada tallafi suka yi a taron samar da dabarun bada tazaran haihuwa.

Gidauniyar Bill da Melinda Gates, asusun UNFPA da kungiyar ‘International Planned Parenthood Federation IPPF na cikin kungiyoyin da suka bada tallafinsu sannan kasashen Benin, Burkina Faso, Ethiopia, Guinea, Kenya, Madagascar, Mali, Mauritania, Niger, Senegal, Tanzania, Togo, Uganda da Najeriya na cikin kasashen duniyan da suka bada nasu baye-bayen domin sanar da dabarun bada tazaran haihuwa.

An tara wadannan kudade domin ganin cewa mata da ‘yan mata sun samu isassun dabarun bada tazaran haihuwa a duniya.

Wani dalilai da suka sa aka tara waɗannan kudade shine domin ganin an samu karin mata kalla miliyan 120 dake amfani da dabarun bada tazaran haihuwa a duniya.

Sakamakon binciken da aka gudanar ya nuna cewa an samu karuwa a yawan matan dake amfani da dabarun bada tazarar haihuwa daga miliyan 40 zuwa miliyan 60

A Najeriya samar da isassun dabarun bada tazarar haihuwa ya taimaka wajen hana mata akalla miliyan 1.9 daukan cikin da basu so, hana mata 705,000 zubar da ciki da ceto rayukan mata akalla 13,000 daga shekarar 2019 zuwa 2020.