Wasu Gurɓatattun Limamai Da Malamai A Kano Sunyi Saukar Alkur’ani Da Nafilfili Da Addu’o’in Wai Neman Bola Ahmed Tinubu Ya Lashe Zaben 2023, Daga Imam Murtadha Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Ya ku bayin Allah! A yau an wayi gari, duk da mummunan halin da arewa da kuma al’ummar yankin arewa muka samu kan mu a ciki na matsalolin rashin tsaro, da rashin zama lafiya, da matsin tattalin arziki, da abubuwa marasa dadi daban-daban, da suka dabaibaye yankin; maimakon al’ummah su mayar da hankali wurin addu’a da rokon Allah ya yaye masu wadannan fitintinu, sai gashi an samu wasu limamai da Malamai a jihar Kano sun gudanar da Sallah, da addu’o’in neman nasara ga Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023, wanda wani dan siyasa ya shirya, ya dauki nauyi, kuma ya biya wadannan mutane masu kiran kan su Malamai.

Wallahi, na samu cikakken bayani, kuma gamsasshe, cewa, Malamai sama da 2,500 ne daga fadin jihar Kano suka halarci wannan Sallar da addu’ar ta munafuncin da munafuntar arewa.

Wadannan makwadaitan Malamai guda 2,500 mayunwata, shedanu, shegu, ‘yan iska, ‘ya ‘yan banza; duk halin da al’ummah ta ke ciki, musamman arewa, sam bai dame su ba, kuma bamu taba jin sun taru sun yi addu’a da rokon Allah ya kawo muna saukin halin da muke ciki ba, amma sai gashi wani dan siyasa ya tara su, ya basu kudi, wai suyi wa Bola Tinubu addu’a, domin yaci zabe, a 2023. Kai jama’ah, Allah wadaran naka ya lalace. Ku sani, sam wadannan mutanen basu cancanci zama Malamai ba. Kawai ‘yan tasha ne, ‘yan gareji, masu sayar da mutuncin al’ummah aka tara!!!

Idan baku manta ba, kwanaki can baya, Tinubu ya raba shinkafa a Kano, saboda ya mayar da mutanen arewa mayunwata. Wadda muka sanya alamar tambaya akan wannan rabon shinkafa da aka yi, muka ce, shin me yasa a can baya bai taba rabon abinci ga mabukatan arewa ba, sai yanzu da yake neman kuri’un su?

Sannan kuma shi Tinubun dai, idan kun tuna, ya kashe kudi, makudai, masu yawa, ya gyara Arewa House. Shine shima wannan aikin da yayi, muka sa masa alamar tambaya. Muka ce shin wai me yasa a can baya duk bai yi wannan ba, sai yanzu da yake neman hawa kujerar shugabancin kasa; wato yana neman kuri’un talakawa, domin ya cuce su ko?

To, koma dai mene ne, muna son wadannan mutane su sani, mu dai a arewa, babu mu, babu Tinubu da ikon Allah!

Kuma wannan ra’ayi nane, kuma fahimta tace, wadda kuma nike da tabbacin, da ikon Allah tayi daidai da ra’ayin mafi yawan mutanen arewa. Kuma mu sani, kowa yana da ‘yancin fadar ra’ayin sa.

Allah ya sawwaka, kuma ya shiryi wadannan mutane, idan masu shiryuwa ne, amin summa amin.

Sannan ina kira ga ‘yan uwa na, ‘yan arewa, da wallahi suyi hankali da duk wani dan siyasa, da zai zo ya yaudare su, ya cuce su, ya zalunce su.

Muna kallon dai halin da muke ciki, musamman mu ‘yan arewa. Ana ta kashe mu, ana sace muna ‘yan uwa ana karbar kudin fansa, ana yiwa matan mu fyade, an hana mu neman ilimi, an hana mu noma da kiwo, amma an kasa daukar matakin kawo karshen wannan bala’i.

Wai kuma muna cikin wannan damuwa, kwatsam, sai wani yazo muna da tallar wani dan siyasar da ba abun da ya taba yi muna na gudummawa ko agaji ko kawo dauki domin magance wadannan matsaloli!

Wassalamu alaikum

Nagode,

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, jihar Kogi, Najeriya. 08038289761.