Bashir Tofa: Ba rabo da gwani ba…, Daga Fatuhu Mustapha

“Ku mu taro mu zaɓi NRC, don kadda mu kai ga taɓewa.”

Na fara gamuwa da Alhaji Bashir Usman Tofa, tun zamanin NRC da SDP. Amma sani na mutum da mutum sai ‘yan shekarun nan, sai dai cikin ƙanƙanin lokaci muka saba, ta zama kamar sanayyar shekara da shekaru ce.

A sanin da na yi masa, mutum ne mai dattako, da yakana, kishi da mutunta mutane. Ba ya shayin faɗar gaskiya ko a kan waye. Ga biyayya ga na gaba, domin ni shaida ne akan wannan. Ya taɓa gaya min dalilin da ya hana shi fito da littafin tarihin sa, ya ce min saboda wasu manya da yake ganin girman su sun hana shi. Da na ce masa ai duk sun rasu, sai ya ce min, idan har bayan rasuwar su zan saɓa musu, to ban ga dalilin da zai sa in ƙi yi a gaban idon su ba. Ya ƙara da cewa ba tarbiyyar mu ba ce, ƙin biyayya ga maganar na gaba. A nan na ɗauki wani sabon darasi na rayuwa.

Wani abin sha’awa game da marigayi Tofa shi ne, duk da nacin da na yi ta yi masa kan littafin, amma bai taɓa nuna ɓacin rai akan na dame shi ba, ko a waya ko gaba da gaba, abin da dai yake gaya min, ba zai haura umarnin da manyan sa suka ba shi ba.

Alhaji Bashir mutum ne karimi, domin ko a yau ɗaya daga cikin abokan sa na kusa, Malam Bilya Bala, ya ba mu labarin ɗaya daga cikin irin karimcin sa, inda ya ce mana ƙarshen ganin sa da shi, watannin baya sun haɗu domin su haɗa kuɗi su taimaka wa wani abokin su. Sai Alhaji Bashir ya ce, shi duk abin da aka tara, zai bayar da linki biyu, haka kuwa aka yi. A lokacin da ya ɗauki sitidiyo ɗin Ruqayya House gaba ɗaya ya bayar ga wasu mawaƙa, na tambaye shi cewa, ba ya ganin ba za su yi amfani da shi yadda ya dace ba? Sai ya ce min, mu dai mun yi abin da ya dace a matsayin mu na iyaye, saura kuma ya rage nasu, su bai wa maraɗa kunya.

Mutum ne mai zurfin tunani da fikirar magana, zama na da shi na fahimci rayuwa na yi karatun rayuwa ƙwarai a wurin sa. Mun tattauna akan ilmin taurari, yadda ake rubutun zube, alaƙar su da IBB, abin da ya haɗa su da Abacha, yadda rikicin na su ya zamar masa alheri, har ya rubuta tarihin musulunci, da makomar Arewa bayan mulkin Buhari, da yadda ya zama Shugaban Jam’iyyar NPN ya na yaro matashi kai har da alaƙar sa da babban abokin sa, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi.

A nan na lura da cewa, bambancin aƙida ko fahimta, bai sa ka ɓata da abokin ka. Domin a lokacin da suka dawo daga karatu a gidan sa Rimi ya zauna, amma sai ga Rimi ya na PRP shi kuma yana NPN, kuma hakan bai taɓa shafar abokantakar su ba, duk kuwa da dagar da aka shaya a tsakanin jam’iyyun guda biyu. Ya kuma sha yi min nasihohi da suka haska min hanya.

Alhaji Bashir, mutum ne mai barkwanci da haba-haba. Zai yi wuya ka same shi, ku yi hira ba ka fito cikin farin ciki ba. Duk saurin da ka ke, idan ku ka fara hira da shi, sai ka manta abin da ke gaban ka. Ya taɓa ba ni wani labari na yadda suka sanya J S Tarka a jirgi daga Lagos zuwa Kano, labari ne mai ban dariya. Da yadda suka fafata da Hassan Sarkin Dogarai a gaban Sarkin Kano Ado, har suka sa Sarki dariya a fada. Da wasu labarai masu ban dariya da na ji a wurin sa. Musamman haɗuwar su da wani attajiri mutumin Kano a Brussels. Wani abin da ba na mantawa kuma yake ba ni dariya a game da shi, shi ne yadda ya dage allankatafar ni abokin sa ne, ba ɗa ba. Abin ya faru ne, da na yi masa waya na nemi izinin zan zo in gaishe shi, sai ya gaya wa masu gadin gidan sa, cewa wani abokin sa zai zo. Wannan ya sanya da na zo, masu gadin suka ce su dai ya ce musu abokin sa zai zo, bai ce ni ba, amma in kira shi a waya.

Da na kira shi, sai ya ce min ai ya gaya musu zan zo, na ce masa su dai sun ce abokin ka zai zo. Sai ga shi ya fito yana musu faɗa, ba ya ce musu abokin sa zai zo ba? Nan aka bar ni da baki a wangale ina kallon ikon Allah.

Tun daga lokacin muke wannan mahawara da shi, shi ya dage akan ni abokin sa ne, nake zuwa mu yi hira, ni kuma na dage ɗan sa ne nake zuwa in ƙaru da ilmin da Allah ya ba shi. Magana ta ta ƙarshe da shi, kusan ‘yan satuttukan baya ne, da na kira in gaida shi, ya ke ce min ba ka kawo yaran ka ba da ka ce suna so su zo su gaida ni. Saboda na gaya masa mun wuce ta ƙofar gidan sa, har su na tambayar gidan waye? Na ce zan kawo ku gaida shi, wani kakan ku ne.

Rayuwar Alhaji Bashir Tofa darasi ce ga matasa, su fahimci cewa ba tarin shekaru ba ne nasarar rayuwa, ilmin da biyayya ga na gaba da kuma son jama’a ita ce nasarar rayuwa. Mutum ne mai kishin addinin sa, bai taɓa yadda da zalunci ba. Dalilin da ya sa ya sha daga da shugabannin Najeriya da dama kenan.

A gaskiya Kano, Najeriya da mutanen Arewa mun yi rashin mutum mai kishin mu da son cigaban mu. Zai yi wuya a mayar da kamar sa.

Allah ya jiƙan sa da gafarta, ya yafe kura-kuran sa, ya sa aljanna makoma.

Kaico, ba rabo da gwani ba!

Fatuhu marubuci ne, masanin tarihin masarautun Arewa ne.