Twitter ta cire kalaman da Buhari ya yi wa ‘yan IPOB barazanar’ gwamnati zata bi da su ta irin yaren da su ka fi fahimta’

Twitter ta cire wasu kalamai da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, inda ya bayyana irin salon da zai bi wajen kawo karshen matsalar tsaro a Kudu maso Gabas.

A ranar Talata ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi barazanar cewa, zai lakada wa masu hankoron tarwatsa Najeriya dukan tsiya.”

Buhari ya buga misali ya abin da ya faru a Yakin Basasa.

“Mu da aka gwabza Yakin Basasa da mu tsawon watanni 30 mu na filin daga, za mu bi da su ta irin yaren da su ka fi fahimta.”

Wannan kalami da Buhari ya yi ya janyo wa kan sa tsangwama da caccaka, inda mutane da dama ke ganin cewa Shugaba Buhari ya yi kasassaba.

Wasu ‘yan Najeriya kuma sun rika rokon Twitter ta cire kalamin tare da dakatar da shafin Shugaba Buhari, saboda munin da kasassabar ta yi.”

A ranar Laraba din nan ce Twitter ta cire furucin na Buhari, tare da kafa hujja da cewa ya karya ka’idar aika sako ta soshiyal midiya.