Martanin gwamnatin Najeriya ga Tiwita, ‘sai ku yi, can ta matse muku’ mun san manufar ku ga Najeriya ba tun yanzu ba – Lai Mohammed

Gwamnatin tarayya ta maida wa kamfanin Tiwita da martani kan cire wani sakon shugaban kasa Muhammadu Buhari ga yan kungiyar IPOB kan barnata kadarorin kasa da suke yi da kaiwa jami’an tsaro hari da suke yi.

Twitter ta cire kalaman da Buhari ya yi, wadanda su ka janyo masa tsangwama ranar Laraba daga shafinta.

Tiwita ta cire wasu kalamai da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi, inda ya bayyana irin salon da zai bi wajen kawo karshen matsalar tsaro a Kudu maso Gabas.

A ranar Talata ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi barazanar cewa, zai lakada wa masu hankoron tarwatsa Najeriya dukan tsiya.”

Buhari ya buga misali ya abin da ya faru a Yakin Basasa.

“Mu da aka gwabza Yakin Basasa da mu tsawon watanni 30 mu na filin daga, za mu bi da su ta irin yaren da su ka fi fahimta.”

Wannan kalami da Buhari ya yi ya janyo wa kan sa tsangwama da caccaka, inda mutane da dama ke ganin cewa Shugaba Buhari ya yi kasassaba.

Wasu ‘yan Najeriya kuma sun rika rokon Twitter ta cire kalamin tare da dakatar da shafin Shugaba Buhari, saboda munin da kasassabar ta yi.”

A ranar Laraba din nan ce Twitter ta cire furucin na Buhari, tare da kafa hujja da cewa ya karya ka’idar aika sako ta soshiyal midiya.

Sai dai kuma ministan yada labarai Lai Mohammed ya bayyana cewa idan ba wata manufa tiwita yake da shi na boye ba, menene illar kalaman da Buhari yayi ga haramtacciyar kungiya kamar IPOB.

” Kowa ya ji irin kalaman da shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu ya ke yi, ya fito karara ya ce a kona ofisoshin yan sanda a kasar nan, ya ce a kashe yan sanda da duk wani soja a kasar nan. Tiwita bai ga hakan ya zama abin kyamata ba sai na shugaba Buhari wanda gargadi ne da jan kunne da yayi wa haramtacciyar kungiyar irin IPOB.

” Su fito karara su gaya mana cewa kawai suma da wata manufa ta su can daban amma ba wai don kalaman Buhari ba.

” Amma tsakani da Allah, idan har gargadin shugaban kasa ga haramtacciyar kungiya a kasar nan zai zama abin tashin hankali ga tiwita, kalaman Nnamdi Kanu kuma ya zama musu abin yabo, toh lallai akwai sake ga yadda tiwita ke yin abinta. Mun sani suna daga cikin wadanda suka tallafawa masu zanga-zangar EndSars a Najeriya. Kuma mun ga yadda suka yi kaca-kaca da kadarorin gwamnati. Sun yi ta ruruta wuta a kai, amma sai gashi a idon mu ‘yan jagaliya suka afka cikin ginin Capitol a Amurka, tiwita suka shiru.

” Babu inda kalaman jan kunne ga wadanda ke kaiwa jami’ an tsaro hari suna kona ofisoshin yan sanda suna kashewa da babbake kadarorin gwamnati ya zama wai kalaman da zai ingiza mutane a yi tashin hankali. Har ya kai ga tiwita ta cire a shafinta. ”