Gidajen Burkutu a Taraba sun fara yajin aiki saboda tsadar itacen dafa burkutu da Dawa

A yau Litinin ne masu sana’ar yin giya da fi sani da burkutu a Jalingo babban birnin jihar Taraba suka fara yajin aikin saboda tsadar Dawa da itace.
Burkutu, wanda ya shahara a jihar, ana yin sa ne gero ko dawa.
Kungiyar masu yin giyar burkuta na jihar Taraba ta koka kan yadda gero da itace suka yi tashin gwauron zabi a jihar da ya sa giyar burkutu ya yi tsada mashaya basu zuwa su rankwale.
Masu sana’ar giyar burkutu sun yi kira da rokon gwamnati ta sa baki a cikin wannan matsala, su samar musu da tallafi domin a samu sauki su ci gaba da sana’ar su.
Naomi Bature ta bayyana cewa saboda tsadar hatsi da itace abokan sana’arta ta sun daina sana’ar. Hakan yasa suka afka cikin tsananin talauci.
” Burkutu na da arha, shine ya sa mutane da dama maimakon su garzaya manyan gidajen giya su sha ta kwalba, su kan zo nan ne su kwankwaɗi kwarya ɗaya ya ishe su, ko kuma su dan hada da na kwalba sai su ji zanzan.
Wani dattijo ya shaida wa waklin mu cewa tun yana ɗan yaro yake kwankwaɗar burkutu, ” gashi yanzu shekaru na 80, lafiya lau ban taɓa yanke rana ɗaya ban sha koda kwarya ɗaya ba. Burkutu duniya ce.
Wasu da dama daga cikin mashaya burkutu sun koka da matsayin da masu yin burkutu suka yi na fara yajin aiki,
” Muna cikin tsananin damuwa matuka yanzu, domin idan babu burkutu komai tsaya mana ya ke yi, su yi hakuri su janye yajin aiki, muna bukatar burkutu matuka.” In ji wasu mashaya