HAJJI 2023: Za a yi aikin Hajji kamar yadda aka saba, ba tare da matsin dokokin Korona ba – Gwamnatin Saudiyya

Mahukunta a kasar Saudiyya sun yi bayyana cewa daga wannan shekara ta 2023 za a dawo da yin aikin Hajjin kamar yadda aka saba yi kafin bullar annobar COVID-19.
Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dr. Tawfiq Al-Rabiah ya sanar da haka a farkon wannan mako.
Ministan ya kuma kara da cewa Masarautar za ta soke ƙayyade shekarun da ake bukata ga mahajjata, bayan shekaru uku na takunkumi don dakile cutar ta COVID-19.
Al-Rabiah ya bayyana haka ne a jiya Litinin a wurin bude taron “Expo Hajj”, taron baje kolin ayyukan hajji da umrah da ake gudanarwa a Jeddah daga ranar 9-12 ga watan Janairun 2023.
Ya ce: “Daga lokacin aikin Hajjin bana za mu ba da damar hukumomin gudanar da hidimomin aikin Hajji daga sassan duniya da su amince da duk wani kamfani da ke da izini don samar da ayyuka ga mahajjata a Masarautar.
“Tare da abokan aikinmu, mun ƙaddamar da dandalin NUSK don sauƙaƙe hanyoyi da haɓaka ayyuka da hidimomi don jin daɗin mahajjata,” in ji shi.
Idan ba a manta ba, tun bayan bullar annobar Korona, Kasar Saudiya ta sauya dokoki da sharuddan aikin Hajji. Wadannan dokoki sun hada da dakatar da baki shiga kasar har na tsawon shekaru kusan uku sannan kuma bayan an dawo sai aka saka dokoki masu tsauri domin kare mutane daga kamuwa da cutar.
Haka kuma gwamnatin kasar sai ta rage yawan mutane da za su shigowa kasar.