Tsohuwar Ministar Buhari ta rasu

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Rahotanni sun bayyana rasuwar Sanata Aisha Jummai Alhassan, tsohuwar Ministar Mata a mulkin Buhari kuma tsohuwar ƴar takarar kujerar Gwamna a jam’iyar APC a jihar Taraba.

Mama Taraba kamar yadda aka fi saninta da shi, ta rasu a wani asibiti mai zaman kansa dake birnin Cairo na ƙasar Masar (Egypt).

A shekarun baya dai tsohuwar Sanatar ta yi fama da ciwon ƙafa wanda ya kai ga aka yi mata aiki.