HADIZA BALA: Yadda Buhari da Amaechi suka karairaya dokar yadda ake tuhuma da dakatar da jami’in gwamnatin Tarayya

Binciken yadda dokar dakatar da babban ma’aikacin gwamnafin tarayya ya nuna karara yadda shugaban kasa da ministan sufuri, Rotimi Amaechi, suka jingine doka a gefe don son ra’ayin su suka dakatar da shugaban Hukumar NPA, Hadiza Bala Usman.

Idan ba manta ba shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun amincewa da dakatar da Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa (NPA), Hadiza Bala-Usman ranar Alhamis bisa shawarar Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

Sanarwar da Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar cikin dare a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an dakatar da Hadiza domin ta kauce a samu damar gudanar da bincike kan zarge-zargen da ogan ta, Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ke yi mata.

Yayin da sanarwar ba ta fayyace irin zarge-zargen ba, Shehu ya ce Buhari ya amince da nada Mohammed Koko a matsayin Manajan Daraktan Hukumar NPA na riko kafin a kammala bincike.

Kafin nadin da aka yi masa na shugabancin riko, Koko shi ne Babban Daraktan Harkokin Kudade na NPA.

Bayan amincewar da Buhari ya yi kan shawarar Amaechi ta a kafa kwamitin bincike, ya kuma amince da nada Daraktan Harkokin Sufurin Jiragen Ruwa na Ma’aikatar Sufuri ta Kasa, a matsayin Shugaban Kwamiti.

Sai kuma Mataimakin Daraktan Harkokin Shari’a na Ma’aikatar Harkokin Sufuri ta Kasa a matsayin Sakataren Kwamitin Bincike.

Sauran mambobin kwamitin dai Amaechi ne zai bayyana sunayen su.

Doka ta nuna karara cewa minista da shugaban kasa ba su da iko kai tsaye na dakatar da shugabar wata hukumar gwamnati ba tare kwamitin gudanarwar wannan ma’aikatar ta san da matsalar ba.

Sannan kuma, dole sai sakataren gwamnatin tarayya ya san da haka kuma shine zai jagoranci kuma ya bada umarnin ayi bincike a kai.

Shine zai ba sanar da shugaban kasa abinda ake ciki kafin nan a san matakin da za a dauka.

Amma kuma duka wadannan hanyoyi wanda doka ta gindaya an wancakalar da su, Minista Amaechi da Buhari sun yi gaban kansu, suka dakatar da shugabar hukumar Hadiza Bala.